Connect with us

KANUN LABARAI

Shirin ‘lafiya’ ya horas da ‘yan jaridu, da kungiyoyin kishin al’umma dabarun aiki

Published

on

Nasiru Yusuf

Shirin lafiya ya horos da yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu kimanin 55 dabarun bibiyar kudaden da ake kashewa bangaren lafiya a matakin farko a nan Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewar anbaiwa ‘yan jaridun horon ne a garin Kaduna daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Oktoba da muke ciki.

Ya yin bada horon an gabatar da makaloli da dama da suke da alaka da yadda aikin zai gudana.

Da yake jawabi ga wadanda aka baiwa horon shugaban shirin Dayyabu Muhammad Yusuf ya ce an shirya horon ne domin a fahintar da su yadda za su bi diddigin yadda ake tafiyar da kudaden da gwamnatin tarayya take baiwa hukumomin lafiya a matakin farko a jihar Kano.

Ya ce matukar ‘yan jarida da kungiyoyo za su sanya idanu yadda ya kamata to shirin zai samu tagomashi, ba kamar yadda na baya suka watse ba

“wannan shi ne karon farko da gwamnatin tarayya ta bayar da kudi kai tsaye ga hukumoin lafiya a matakin farko.

“A wannan lokacin tallafin ba zai biyo ta hannun ayyukan yan majaisa ba, kudin kai tsaye za a baiwa asibitoci.

“Kuma akwai bukatar duk wani karamin asibiti da aka baiwa kudin ya yi amfani da shi yadda ya kamata, musmman m gyaran gine-ginen su, da kuma walwalar ma’aikata.” A cewar sa.

Malam Yusuf ya kuma  koka kan cewar kimanin jihohi 30 na kasar nan basu yi amfani da kudin tallafin ba tun na shekarar 2018.

Hakan ya faru ne  sakamakon rashin amincewa da ka’idojin yin amfani da su da zai yi dai-dai da tsarin dokar da ta shafi al’amuran lafiya da majalisar kasa ta gano.

Sa dai ya ce da wannan sabon tsarin,  akwai kyakyawan fatan jihohi da dama za su fara aiwatar da shirin.

Ya kuma ce ana sa ran yan jarida za su fara sanya idanu akan ayyukan da zarar an fara gudanar da shi domin tabbatar da anbi ka’idojin da suka da ce.

Da suke gudanar da jawaban su daga bangaren kungiyoyin kishin al’umma da kuma ‘yan Jaridu Hajiya Maimuna Muhammad da Ibrahim Musa Giginyu sun bukaci wadanda aka baiwa horon da su yi aiki da abin da suka koya.

Yayin horon shugaban Hukumar lafiya a matakin farko na jihar Kano ya gabatar da Makala mai muhimman ga ci gaban aikin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending