KANUN LABARAI
Ministocin Kano biyu sun bukaci ‘Sarki’ ya taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya
Mukhtar Yahya Usman
Ministocin Kano biyu Sabo Nanono da Bashr Salihi Magashi sun bukaci mai markataba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen zanga-zangar matasa a jihar Kano.
Kano Focus ta ruwaito ministocin na mika rokon na su ne ya yin da suka kaiwa sarkin ziyarar aiki fadarsa a ranar Litinin.
Ministocin biyu sun bukaci sarkin da ya ba da tasa gudunmawar wajen kawo karshe matsalar da ke addabar kasa a halin yanzu a matsayin sa na mai son zaman lafiya da kwanciya hakali.

Sun ce masarautun gargajiya na taka rawa kwarai da aniya wajen wayar da kan al’umma, a don hakan ne ma suka nemi hadin kansa wajen fadakar da su illar al’amarin.
Baka da ‘yancin da ya fi mallakar katin dan kasa-Sarkin Karaye
Farfesa Danbatta ya ziyarci malaman Kano, ya roki a zauna lafiya
Zaman lafiya ke kawo ci gaban kowacce al’umma- Danbatta
Sun kuma ce akwai bukatar sarkin ya wayar da kan matasa su rungumi sana’o’in dogaro da kai da gwamnatin tarayya ta fito da su don ciyar da kansu gaba.
Da yake nasa jawabin sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci ministoci da suje garuruwansu su kuma taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya.
Ya kuma sha alwashin ba su hadin kai bisa kokarin su na ganin an kawo karshen zanga-zangar da ke faruwa a tsakanin matasa.
Ya ce Kofarsa a bude ta ke koda yaushe domin bada shawarwari da zarar an nemeshi.
Sarkin ya yi addua’ar neman zaman lafiya ga kasa baki daya, kuma ya roki Allah da ya kawo karshen cutar COVID-19 a kasa baki daya.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
