Connect with us

KANUN LABARAI

Ko jam’iyyu a Kano za su baiwa matasa dama a zabukan da ke tafe

Published

on

Aminu Abdullahi

Matasa a jihar Kano sun koka kan yadda siyasar uban gida da kudi ke neman kassara musu mafarkin su na zama zababbu a matakai daban daban na shugabancin kananan hukumomi dake tafe.

Jaridar Kano Focus tayi nazari kan yadda matasa daga kananan hukumomi daban daban suka fito don ganin an zabe su a kujerar shugabancin karamar hukuma ko ta kansila.

A baya dai ba safai aka saba ganin matasan na tsayawa takara ba, yayin da kuma wasu ke shan kayi tun a zaben fidda gwani na cikin gida, wasu kuma akan nemi da ayi sulhu domin janyewa wadanda suka dara su shekaru kuma suke da abin hannu.

Nuradeen Babani Musa mai shekaru ashirin da biyar dake takarar shugabancin karamar hukumar Tudun Wada a jam’iyyar A.P.C ya ce  rashin isassun kudade da iyayen gida yasa tun a zaben fidda gwani da jam’iyu ke gudanarwa ake watsi dasu.

Ya ce wani lokacin akan tilasta musu da su janyewa wadanda shekarun su sukaja kuma suke da abin hannu.

Ya kara da cewa barin matasa da ‘yan siyasa suke yi a baya shiyasa ya fito takarar shugabancin karamar hukumar amma kuma da alama gwamnati tana da wanda takeso ya tsaya takarar.

“Akwai matasa da yawa da muka fito takarar tare dasu, akwai kuma manya masu shekaru da kudi, da alama kuma a cikin manyan za a bawa wani takarar.

“Yawanci wadanda suka haura shekaru hamsin ne ke tsayawa takarar, yanzu mun fito za a yi zaben fidda gwani amma alamu na nuna cewa jam’iyya nada wadanda suke so,” inji shi.

Haka zalika wani dan takarar Kansila a karamar Hukumar Rano a jam’iyyar A.P.C mai shekaru ashirin da biyar Usman bn Usman cewa yayi bai kamata manyan da suka haura shekaru talatin su  fito takara a kananan hukumomi ba.

Yana mai cewa kamata ya yi su zama masu bada shawara kawai ga matasa kasancewa suma matasa na da rawar da za su taka don kawo canji a cikin al’umma.

Sai dai ya ce da yawa idan matasa suka fito takara akan nemi da ayi sulhu da su,  ba tare da an gudanar da zaben cikin gida ba.

Zaben Kananan hukumomin Kano zai lakume sama da Naira miliyan dubu biyu

Za mu bada cikakken tsaro yayin zaben kananan hukumomi a Kano-Kwamishinan ‘yan sanda

Rashin filayen wasanni na kara sanya yara da matasa zama dakikai a Kano

Ya kara da cewa jam’iyar da yake takara bata barin kowa yasiyi fom na tsayawa takarar fidda gwani a karamar hukumar Rano, maimakon haka sai dai jam’iya tayi sulhu a tsakanin ‘yan takara tare da siyawa wanda aka zaba fom din tsayawa.

“Jam’iyya tana yaudarar ‘yan takara ne ta hanyar cewa sulhu alkairi ne daga nan kuma sai a zabo bara gurbi a dora wanda ba zai yiwa al’umma komai ba.

“Kaga a mazabarmu sulhun ma gagara ya yi karshe jam’iya ce kawai ta dauko wanda takeso tace yayi takara,” a cewar sa.

Nura Abdullahi mai shekaru ashirin da uku dake takarar kansila a tsohon gari dake karamar hukumar Tudun Wada a jam’iyyar P.D.P ya ce akwai alamun cewa jam’iyyar sa za ta tsaida shi a matsayin dantakarar kansila.

Ya ce duk da rashin kudi isassu ga matasa amma a wannan karon alamu na nuna cewa za a samu matasa cikin shugabancin karamar hukuma dana kansiloli.

Nura Abdullahi ya kara da cewa matukar aka baiwa matasa dama to tabbas za su kawo canji kan yadda ake tafiyar da tsarin kananan hukumomi a jihar nan.

Gwamnati ke yin nune

Shugaban jam’iyyar A.P.C dake mazabar Rano ta tsakiya a karamar hukumar Rano Mukhtar Dahiru yace ko kadan shugabanin jam’iyya basa hana matasa tsayawa zaben fidda gwani.

Ya ce masu mulki dake da ruwa da tsaki a gwamnati suke yin uwa da makarbiya ga zabukan kananan hukumomi domin kuwa suke nuna wanda suke so ya tsaya takara.

Ya kara da cewa a karamar hukumar Rano dan majalisar jihar na tarayya Kabiru Alhassan Rurum shike nuna wanda za a tsayar a matsayin kansila ko shugaban karamar hukumar yankin.

Mukhtar ya kuma cewa dabi’ar nune da dan majalissar keyi yasa duk wanda aka zaba a matsayin shugaban karamar hukuma ko kansila basa ganin shugabannin jam’iyyu da kima.

“Wani lokacin ma ba ayin sulhu kawai wani babba a gwamnati ne zaice ga wanda yake so kuma ba yadda za a yi shi za a tsayar a matsayin dan takara na jam’iyya,” a cewar sa.

Sulhu muke yi

Ya yin zantawar sa da jaridar Kano Focus mai rikon shugabancin jam’iyyar PDP na jihar Kano Danladi Umar Abdulhamid cewa ya yi jam’iyyar PDP bata yin nune.

Ya ce hasalima jam’iyya ce dake baiwa matasa maza da mata dama don su nuna tasu kwarewar a siyasance domin ciyar da kasa gaba.

Ya kara da cewa suna gudanar da zaben fidda gwani ga duk kan ‘yan takara sannan wanda yaci sai bashi.

Saidai wani lokacin sukan yi sulhu ga ‘yan takarar don rage musu kashe kudi.

“Wani lokacin idan aka samu akayi sulhu tsakanin juna yakan fimana sauki a matsayin mu na yan adawa saboda kada dan adawa ya kashe kudi kuma idan yaci jam’iyya mai mulki ta hana shi.

“A matsayina na shugaban jam’iyya a yanzu ina iya yimaka rantsuwa banda wani dan takar,  hakama yan kwamitina na yi zama dasu sunyimin rantsuwa cewa basu da wani dan takara a da zasu nuna,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Malaman Tijjaniyya na Kano sun kai wa Khalifa Muhammad Sanusi ll mubaya’a

Published

on

Nasiru Yusuf

Majalisar Shura ta Dariqar Tijjaniyya ta Jihar Kano ta kai wa Maimartaba Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II mubaya’a bisa nadin da aka yi masa na babban Khalifan Shehu Ibrahim Inyass a Nigeria.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Malaman sun yi wa Malam Muhammadu Sanusi ll mubaya’ar ne ranar Asabar karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Awaisu Limanci.

Malaman da suka kai ziyarar mubaya’ar sun hada da Khalifa Tuhami Shehu Atiku da Shehi Shehu Maihula da Imam Muhammad Nura Arzai da kuma Sheikh Dayyabu Dan Almajiri.

Sauran sun hada da Khalifa Hassan Sani Kafinga da Khalifa Bashir Musa Kalla da Khalifa Fatihi Uba Safiyanu da Khalifa Kamilu Yalo da Sheikh Tijjani Maisalati Indabawa da kuma Sheikh Kabiru Zango.

Tawagar kuma ta kunshi zuriyar Shehu Ibrahim Inyas mazauna Kano karkashin jagorancin Sayyada Rahama Ibrahim Inyas.

Continue Reading

Hausa

Majiyyata sun koka kan yajin aikin likitoci a Asibitin Malam Aminu Kano

Published

on

AKTH

Aminu Abdullahi

Yajin aikin likitoci masu neman kwarewa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ya jefa marasa lafiya cikin mawuyacin hali.

A zagayen da Kano Focus tayi ta gano yadda yajin aikin likitoci masu neman kwarewa ya gurgunta harkokin kula da lafiyar majiyyata a asibitin.

Wani majinyaci mai suna Abba Shehu ya ce mafi yawansu ‘yan’uwansu ne ke kulawa da su.

Ya kara da wasu kuwa an salleme su zuwa gida sakamakon karancin wadanda za su kula da su.

Ya kara da cewa a ya yin da aka shiga kwana na uku ana yajin aikin ya gaza samun allurar da yakamata a yi masa.

“Typhoid ke damuna, a da ina samun kulawa sosai, sa6anin yanzu. Iya magunguna kawai na sha, amma ba bu wanda zai yi min allura,” a cewarsa.

Maryam Yusuf cewa ta yi, ta fara rashin lafiya ne daga ciwon kai wanda har takai ga ta kwanta.

Ta kara da cewa tazo ganin likita, amma cikin rashin sa’a aka ce bai zo ba, duk da cewa ciwon yana damunta.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa reshen asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Mujahid Muhammad Hassan, ya ce ba za su koma bakin aiki ba har sai an biya musu bukatunsu.

Ya ce kaso saba’in da biyar na likitocin asibitin suna cikin kungiyar, kuma sune suke gudanar da yajin aikin.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatarsu ta kara kudaden ‘hazard allowance’ da suka yi ‘yarjejeniya a shekarar da ta gabata.

“Kudin da ake baiwa ma’aikatan lafiya na ‘hazard allowance’ bai wuce dubu biyar ba a wata.

“A kwai likitocin da ake cewa ‘house officers’ ba a biya su albashinsu na watanni uku ba, shima muna bukatar a biyasu dukkan hakkokinsu kafin mu janye yajin aiki,” a cewar sa.

Ya kuma ce dole ne a biya su ‘allowance’ kaso hamsin cikin dari na cikakken albashin kowane ma’aikaci.

Ya ce “Dole ne a biya mu bashin ‘allowance’ na yaki da annobar COVID-19 a manyan asibitocin jihohi.”

Continue Reading

Hausa

Rashin kasuwa ya sa ma su sayar da zo6o komawa sana’ar kunu

Published

on

Aminu Abdullahi

Kasuwar zobo da kunun aya da lemo da kuma lamurje na neman 6acewa a jihar Kano biyo bayan hana sayar da kayan hadin lemukan da gwamnatin jihar tayi.

Kano Focus ta ruwaito yadda wasu ma su sana’ar zo6o suka koka bisa yadda a yanzu sana’ar ke neman rugujewa sakamakon rashin masu siye.

Talatu Hassan ta ce ada tana yin cinikin zobo na naira dubu uku a kowace rana saidai a yanzu dakyar take sayar da na Naira dari biyar sakamakon rashin ma su siye.

Ta kara da cewa kayan hadin suna da matukar tsada kuma ba ko ina ake samun su ba sakamakon haramta sayar da su da akayi.

” Idan munje kasuwar ma a boye ake siyar mana da su wani lokacin ma haka muke dawowa ba tare da mun siyo ba.

” Jarina ya karye kowa yana jin tsoron siya don kada ya kamu da wata annoba a zahirin gaskiya muna cikin wani hali,” a cewar ta.

Aisha Lawan ta ce tana saidai zo6o da lemo da kunun aya na Naira dubu hudu kafin bullar annobar da ake zargin sinadaren hadawa ne suka haddasata.

Saidai ta ce a yanzu tana sayar da iya zo6o ne kawai ba kuma tare da ta sanya masa sinadaren da ta saba sawa a baya ba.

“Yanzu ba a siyar dasu sai ansha wahala ake samu ina yin zo6o na dari uku ko biyar ne a kullum shima da siga kawai nake hadashi.

“Gaskiya a yanzu yafi tsada tunda ba bu kayan hadi dake saka shi zaki, kawai iya dafaffen Zobo ne da sikari,” inji ta.

Ta kuma ce kamata yayi gwamnati ta samar da doka mai tsauri da za a hukunta duk wanda aka kama yana saida sinadaren da suka lalace maimakon haramta siyarwa gaba daya.

” Kaga yanzu azumi na zuwa kuma mun fi yin ciniki da azumi fiye da yadda muke yi a baya, don ni na yanke shawarar fara tuyar awara tunda yanzu ba bu kasuwar zo6o,” a cewar ta.

Rukayya Abdullahi ta ce yanzu ta koma sana’ar sayar da awara da Kunu saboda daina siyan zobo da aka yi.

“Tun daga lokacin da aka ce annobar nan ta bulla kuma a sanadiyyar kayan hadin zobo, nake tafka a sara.

” Dole ce ta sanya na koma sana’ar saida kunun tsamiya da awara domin idan na zauna ba bu mai ba ni,” inji ta.

” ya”ya na uku kuma mahaifinsu ya rasu shekaru biyar da suka gabata,” a cewar Rukayya.

A na su bangaren wasu mutane sun bayyana fargabar da suke da ita na shan Zobo.

Saifullahi Usman ya ce duk da cewa mahukunta na alakanta annobar data faru da shan zobo wanda aka hada da sinadaren da suka lalace amma har yanzu yana siya ya sha.

Ya ce a yadda ake zafi a gari yana bukatar abinda zai sanyaya masa makoshi mai zaki kuma bashi da halin da zai sayi lemo dan kamfani wanda hakan tasa yake cigaba da siyan dan hadi,” a cewar sa.

” Ni ba zan iya kashe fiye da naira dari ba don kawai nasha lemon roba na kamfani na gwammace nasha zobo na Naira hamsin na hada da abincin dari da hamsin.

Kullum sai na siya amma dai yawan sa bai kai na da, da nake siya ba,” inji shi.

Zainab Jibril ta ce daga lokacin da annobar ta bulla zuwa yanzu bata kara shan wani abu da tasan ana hadawa da sinadarin ba.

Ta ce wani lokacin ma takan gwammacewa ta hada da kanta maimakon siyan na waje.

“ina fata a shawo kan wannan matsala kafin azumi, don al’umma za su shiga cikin wani hali matukar aka tafi a haka,” inji ta.

Continue Reading

Trending