Connect with us

KANUN LABARAI

Korar Rahama Sadau ba zai tsarkake ‘yan fim ba-Jaruma Farida Jalal

Published

on

Aminu Abdullahi

Jarumar fina-finan hausa Farida Jalal ta ta ce hukuncin da kungiyar masu shirya fina -finan Hausa ta MOPPAN ta yanke na korar Rahma Sadau sam bai dace ba.

Farida Jalal wacce ta kasance tsohuwar jaruma a Kannywood ta bayyana hakanne yayin tattaunawarta da jaridar Kano Focus a ranar Litinin.

Ta ce ba wannan ne karon farko da aka kori Rahama Sadau ba, a cewarta za su sake dawo da ita daga baya komai daren dadewa.

Ta kara da cewa kamata ya yi shugabanin kungiyar su samar da hanyoyi da za su dinga ladabtar da duk wani mutum da yake aikata laifi irin na Rahma amma ba kora ba.

Farida Jalal ta ce al’umma ba za su daina kallon  Rahma Sadau a matsayin jarumar masana’antar ba.

Kuma koda ta sake aikata wani laifin za a cigaba da alakanta ta ne da masana’antar.

“A da an kore ta kuma an dawo da ita, yanzun ma wannan kora ba za ta yi aiki ba, ” a cewar ta.

Jarumar ta kara da cewa kamata ya yi jaruman masana’antar su hade kansu tare da ciyar da masana’antar gaba, ba wai jifan juna da munanan kalamai ba.

“Abin takaici ne yadda wasu daga cikin mu suka dinga aibanta jarumar da yin tsinuwa gare ta bayan kuma kowannen mu mai laifi ne.

“Ta nuna nadamarta da ya kamata a ce mun yafe mata, muna yiwa Allah laifi kuma yana yafe mana matukar muka nemi gafarar” a cewar ta.

Jaruma Jalal ta ce komai ya faru Rahma Sadau ce ta jawowa kanta amma tunda ta tuba kamata ya yi a yafe mata.

Ta kuma yi kira ga jaruman masana’antar da su hade kansu tare da yin amfani da koyarwar addinin musulunci a duk kan al’amuran su na yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending