Connect with us

KANUN LABARAI

Dalilan da ke sa iyaye yiwa ‘ya’yansu auren dole

Published

on

Wani masani kan zamantakewar dan adam a jami’ar Bayero dake nan Kano Malam Aminu Dambazau ya ce iyaye na yiwa ‘ya’yansu auren dole ne bisa dalilai da dama.

Malamin yayin zantawarsa da jaridar Kano Focus ya zayyana dalilai hudu a matsayin manyan dalilan da ke jawo auren dolen ga yara mata.

Ya ce dalilan sun hadar da kwadayi da talauci da kuma jahilci sai kuma al’ada.

Ya ce galibin  matan da shekarun su suka haura a shirin zuwa talatin sune suka fi fuskantar kalubalen auren dole.

Talauci

A cewar malamin iyaye suna yiwa ‘ya’yan su auren dole ne domin kubuta daga talauci.

Ya ce wasu iyayen kan zabi su aurar da ‘ya’yan su mata ga masu kudi domin dauke musu wahalhalun kudaden da za su kashe yayin aurar da ‘ya’yan nasu.

“Wani mahaifin yana tirsasawa ‘yar sa auren mai kudi koda kuwa bata son sa.

“Dalili kuwa shi ne wani zai dauki nauyi duk kudin da za a kashe a bikin.

“A karshe sai kaga yarinya tashiga wani hali wanda bai kamata ba,”

Jahilci

Ya kuma ce karancin ilimi da wasu iyayen ke dashi na taka rawar wajen kara ta’azzara dabi’ar auren dole.

Ya ce idan da ace iyaye sun san irin matsalar da hakan zai haifar bayan yin auren, ko kadan ba za su yiwa ‘ya’yan  su ba.

Malam Danbazau ya ce wasu iyayen na da karancin ilimin fahintar menene ma auren dole da hakan ke sa su aurar da yaransu ga wanda suke bukata ba tare da la’akari da matsalar da hakan zai haifar ba.

Kwadayi

Malam Aminu Dambazau ya ce galibin wasu iyayen na yiwa yaransu auren dole ne saboda kwadayin abin duniya kawai.

 

“Akwai iyayen da kwadayin abin duniya ke sa su yiwa ‘ya’yansu mata auren dole.

“Za kaga suna da rufin asiri amma idan wani yafito daga babban gida, ko yafi su arziki to a kokarin alakanta kansu da mutumin sai su aurar da ‘ya’yansu gareshi koda kuwa basa son sa.”

Dambazau ya ce neman suna da son a rakabu da jikin masu da shi na taka rawar gani wajen yin auren dole.

Malamin ya ce aurar da ‘ya mace ga wanda bata so, take hakkin dan adam ne da cin zarafinsa da ya zama wajibi a kawo karshen dabi’ar..

“Wasu ‘ya’yan kan kashe kansu koma su kashe wanda aka aura musu ta hanyoyi ma banbanta.

Al’ada

Haka zalika Dambazau yace wasu kabilun al’adarsu ce zabawa ‘ya’yan su miji ko matar da za su aura ba tare da sanin su ba.

A cewarsa Hausawa sun dade da dabi’ar  yiwa ‘ya’yansu auren dole, da a karshe hakan ke haifar da gaba a cikin iyali.

“Akwai matan dake sanadiyar mutuwar mazajensu ta hanyoyi daban daban sakamakon gina auren ba bisa ka’ida ba”

Ya kuma ce babu yadda za a yi ma’aurata su zauna lafiya matukar ba ayi auren bisa soyayya ba.

Ya ce wasu matan kan cigaba da mu’amala da samarin su nada duk kuwa da cewa akwai aure a kansu.

“A karshe sai kaga yarinya da aurenta amma tana karuwanci da wani namijin a waje,

“Hakan kuma ka iya sawa ta dauko wata cutar da za ta shafawa mijin ta na gida,”

Haka zalika ya ce koda an haifi ‘ya’ya basu cika samun kulawa yadda yakamata ba daga gurin mahaifiyarsu.

Ya kuma shawarci masu yin aure da su kauracewa auren wadanda suka nuna basa kaunarsu domin gujewa matsalar da kaje tazo.

Auren dole na tafiyar da farinciki na har abada

Wasu mata da jaridar Kano Focus ta zanta da su da suka tsinci kansu cikin auren dole, sun ce auren ya tafiyar musu da farinciki na har abada.

Hadiza Umar wata mata ce da aka yiwa auren dole ta ce duk da Allah ya albarkanceta da ‘ya’ya uku amma ta rasa farin cikinta tun daga lokacin da mahaifiyyarta ta aura mata wanda bata so.

Hadiza  mai shekaru Talatin  tace tana da wanda takeso da har sunyi alkawarin yin aure da zarar ta kammala karatun digiri.

Amma daga baya mahaifiyyar ta ta gabatar mata da wani mutum na daban a matsayin wanda zata aura.

Ta ce mahaifinta ya rasu wanda hakan yasa mahaifiyyarta itace kadai keda iko akan su.

“Saurayina na farko mai suna Aliyu Adam munyi matukar shakuwa kuma yana da rufin asiri daidai gwargwado.

“Ya kuma nemi ya turo magabatansa don ayi magana amma sai mahaifiyyata tace tana da wanda takeso ta aura min.

Ko menene mahangar addini

Wani malamin addinin musulunici a nan Kano da ke unguwar Sharada Muhammad Umar Sharada ya ce ba dai-dai bane iyaye su dinga yiwa yayansu auren dole.

Haka ya ce tilastawa yara mata fito da miji bayan basu da tsayayye ba dai-dai bane, kuma baya cikin koyarwar addini.

Malamin ya ce Allah da kansa ya ce kowanne  al’amari a kididdige ya ke kuma yana da lokacin faruwarsa.

A don haka ne ya ja hankalin iyaye da su dinga bin koyarwar addinin musulunci a koda yaushe.

A cewar sa akwai tarin matsaloli matukar akayi auren da ya saba koyarwar addinin musulunci.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina

Published

on

 

Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.

 

Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.

 

Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.

 

Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).

 

“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.

 

Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.

 

“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.

 

“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.

 

Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.

Continue Reading

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Trending