Connect with us

KANUN LABARAI

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da matashi da ya shafe awa 7 a cikin kwata

Published

on

Zulaiha Danjuma

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta kubutar da wani matashi da ake zargin mai tabin hankali ne da ya shige kwata a Unguwar Kabara dake birnin Kano, da ya kwashe sama da awanni bakwai.

Kano Focus ta ruwaito matashin da har yanzu ba a’a kai ga tantance sunansa ba ya shiga kwatar ne da misalign karfe bakwai na daren ranar litinin ba a kuma samu nasarar kubutar da shi ba har sai misalin karfe daya zuwa biyu na dare.

A cewar shaidun gani da ido matashin ya shiga kwatarne inda ya ce ba zai fito ba har sai Buhari ya sauka da ga mulki.

Sai dai maganganun basu da tabbasa domin kuwa ba a ji ta baki matashin ba a cewar rundunar ‘yan sanda.

Sale Uba Kabara da ake yiwa lakabi da Waga na daya daga cikin wadanda suka yi yunkurin kubutar da matashi, ya  ce sun dauki kusan awanni shida zuwa bakwai suna yunkurin fito da shi daga kwatar amma ya kekasa kasa ya ki fitowa.

Ya ce jami’an Kwan-kwana da na  Civil Defense sunje wurin, amma dukkansu basu samu nasarar kubutar da shi ba.

Har sai da jami’an ‘yan sanda suka halarci wurin sannan suka samu nasar kubutar da shi cikin dare.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa suna samun labari suka garzaya wajen da rundunar su ta kan kace kwabo domin kai masa dauki.

Abdullahi Haruna mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce bayan daukan lokaci wajen ganin an lallabashi ya fito, da ga bisani sun fada cikin ramin suka kuma fito da shi.

Ya ce bayan sun fito da shi ne kuma suka yi masa wanka, inda suka fara yi masa tambayoyi sai dai sun fahince kamar yana da tabin hankali.

Kiyawa ya ce ko da ya ke ba a tabbatar da rashin hankalin nasa ba amma dai tuni aka fara gudanar da bincike.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending