KANUN LABARAI
Rubutun ‘ajami’ akan kudi ba musuluntar da Najeriya ba ne-CBN
Mukhtar Yahya Usman
Babban bankin kasa CBN yace ko kadan rubutun ajami akan kudin Naira ba yana nufin musuluntar da kasa ba ne kuma ba zai cire ba.
Kano Focus ta ruwaito babban bankin kasar, na mayar da martani ne kan karar da wani lauya mazaunin Legas ya shigar gaban kotu yana mai bukatar da a cire rubutun ajami a jikin kudaden kasar nan.
A cewar Lauyan Abiola Lawan rubutun ajamin dake kan kudin Najeriya ba ya nufin wani addini ko hulda da larabawa.
Lauyan na CBN ya caccaki lauyan kan ikirarin cewa rubutun ajamin barazana ce ga yancin addini a Najeriya.
“Rubutun dake kan takardar kudin kasar nan ba barazana bane ga kasa kuma bai sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba.”
“Tun shekarar 1973 da aka canza kudin Najeriya daga Fam zuwa Naira ake amfani da rubutun Ajami.”
“Rubutun Ajami ba alama bane na Musulunci, an yi ne domin saukakawa wadanda basu iya karatun Boko ba wajen kasuwanci,”
Idan za a iya tunawa wani lauya mazauni jihar Legas, Malcom Omirhobo, ne ya shigar da kara gaban babbar koto a jihar Legas yana mai neman da a tilasawa babban bankin kasa ya cire ajami a jikin kudi.
Lauyan ya ce, rubutun yaren larabcin dake jikin Naira na nuna cewa Najeriya kasar Musulunci ce alhalin ba haka take a kundin tsarin mulki ba.
Lauyan, wanda yace shi bai san ma’anar rubutun ajamin ba, ya bukaci kotu ta cire kuma ta maye gurbinsa da na Turanci.
Ya ce ko kuma a maye gurbinsa da harsuna uku mafi shahara a Najeriya wato Hausa, Yoruba ko Igbo.
A cewar lauyan, da rubutun ajamin, CBN ta saba sashe 10 da 55 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.