KANUN LABARAI
An Kama masu amfani da layin wayar da jama’a ke yarwa suna sace kudi a banki
Aminu Abdullahi
Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Kano ta kama wasu matasa da ake zargi da yin amfani da layukan wayar jama’a su sace kudaden mutane a asusun ajiyar bankuna.
Kano Focus ta ruwaito daya daga cikin wadanda aka kama Musbahu Balarabe na cewa suna siyan layikan waya ne da jama’a suka daina amfani da su sannan sunemi adawo musu dasu daga kamfani a matsayin nasu da suka bata.
A cewarsa suna yin wani abu da ake cewa ‘on demand’ akan layin, da hakan zai nuna musu ko akwai asusun ajiya na banki akan layi.
Ya ce da zarar sun fahinci mai layin yayi rijista da shi akan wani asusun ajiya to sai suyi amfani da shi wajen satar kudin.
Shima daya daga cikin wadanda ake zargin Sadiq Sani mai shekaru ashirin da bakwai ya ce bayan sun kwashe kudin asusun da suka gano sai su kama Otel wanda a can ne suke kashe kudin da suka samu.
A nata bangaren rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano ta ce an kama matasanne bayan da suka sace kimanin milyan biyar a asusun ajiya na banki.
Mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa yace akwai irin wadannan matasa da dama da suke amfani da kwamfutocin, suna damfarar mutane.
Abdullahi Haruna mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye wajen kulawa da layikansu da kuma wayoyin su na hannu.
Ya kuma shawarci al’umma dasu rinka kulawa da layikan ‘yan uwansu da suka rasu.
A cewarsa mafiya yawan masu wanna ta’ada sun fi amfani da irin layukan wajen sace kudaden mutane.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.