KANUN LABARAI
‘Yan sanda a Kano sun kama dan sahun da ke sauke fasinja ya gudu da kayansu
Aminu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani direban adai-daita sahu mai suna Muhammad Muhmmad bayan da ya tsere da kayan fasinjoji.
Kano Focus ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Na’ibawa ‘yan Lemo a ranar Litinin.
Hadiza Hashim wacce dan sahun ya tserewa da kayan ta ce dan sahun ya shammace ta ne ya kuma gudu da kayan da ta yi cefane.
Kayan su hadar da buhun fulawa da katan din taliya da magi da kuma shaddoji da yaduka.
Ta ce direban adaidaita sahun ya kashe baburin nasa ne da sunan ya mutu a daidai lokacin da suka isa gadar Na’ibawa mai hawa uku.
Sai dai ta ce lokacin da ya ce su sauka domin ya duba me ya kashe masa baburin sai tayi kokarin haddace lamabar da ke jikin baburin.
“Ya nemi mu tura masa baburin, sai da muka tura masa ne ya shiga da gudu ya kunna abinsa ya wuce ya barmu nan tsaye.
“Amma lokacin da yace mu sauka nayi sauri na rike Lambar baburin nasa.
“Bakar nambar itace 6543 Gwale yayinda kuma plate nambar sa itace Adamawa Yola 194 QA.
“Lokacin da ya gudu sai nayi salati sai kuma naji wani huci mai zafi ya lullube ni daga nan kuma bansan inda kaina yake ba.
“A she suma nayi daga nan kuma sai mai gidana yazo ya dauke ni ya kaini asibiti,” a cewar ta.
Muhammad Ahmad Muhammad shi ne direban adai-daita sahun da ya ce son zuciya ne yasa ya aikata abinda ya yi sai dai ya yi matukar nadama.
Muhammad mai shekaru talatin da tara mazaunin unuguwar Kabuga ya ce bayan da ya gudu da baburinne sai kuma jami’an ‘yan sanda suka bibiyi nambar baburin.
Hakan ta sanya suka kama kaninsa sa’ilin da yake aiki da baburin wanda daga nanne aka kama shi.
Ya ce lokacin da aka kamashi ya riga ya siyar da fulawa da taliya sannan kuma ya kai a jiyar ragowar kayan gurin abokin sa.
“Yanzu duk an kamomu dani da kuma wanda na kaiwa a jiyar ragowar kayan.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce jami’ansu ne suka yi bincike saka kuma kamashi.
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce tuni aka kammala bincike kuma za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.