Connect with us

KANUN LABARAI

Murhun girki: Kishiya ta babbake abokiyar zamanta a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wata mata mai suna Hannatu Rayyanu ta kona kishiyarta da ruwan zafi a garin Darki dake karamar hukumar Wudil biyo bayan sa-in-sa kan murhun dafa abinci.

Kano Focus ta rawaito cewa tun da fari dai sa-in-sa ce ta shiga tsakanin Hannatu Rayyanu da kishiyarta mai suna Fa’iza Sani a ranar Laraba.

Da hakan ya kai ga Hannatu ta salube jikin a bokiyar zaman nata da tafasheshen ruwan zoborodo tun daga kanta har zuwa kaurin ta.

Da take zantawa da Kano Focus Fa’iza ta ce ta nemi kishiyarta ne da ta bata murhu  domin ta dorawa yara da mai gidan abinci.

Bayan da ta tambayeta ne kuma sai bakaken maganganu suka biyo baya, da hakan ya kaisu ga dambatawa.

Hakan yasa Hannatu ta dauko tafasheshen ruwan zobo tayi mata wanka dashi.

“Na fito kawai ta kwaromin ruwan zobon a jikina, gaba daya fuskata da hannuna da kuma bayana duk sun kone”. A cewar ta.

Ta kara da cewa bayan da aka dawo da ita ne daga asibiti sai kishiyar ta ta ta sake gayyato ‘yan uwan ta domin su lakata mata duka.

Sai dai da jaridar Kano Focus ta tuntubi mijin matan biyu mai suna Abubakar Yusuf ya ce lokacin da suka dambata ya fita kasuwa.

Ya ce bai samu labariba ko kadan har sai da ya dawo daga kasuwa ya iske halin da gidan nasa ke ciki.

Ya ce ba zai yi karin bayani ba game da batun har sai abinda bincike ya bayyana, tunda dai maganar na gaban yan sanda.

Sai dai munyi kokarin jin ta bakin wadda ta aikatai ta’asar amma hakan mu bai cimma ruwa ba kasancewar tana hannun yan sanda ana kuma tsaka da bincike.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending