KANUN LABARAI
Rashawa: An kama ma’aikacin kotu da ke karbar kudade da sunan al’kali a Kano
Aminu Abdullahi
Wani ma’aikacin kotun Kofar Kudu dake karamar hukumar birni a nan Kano Bahir Muhammad ya fada hannun jami’an tsaro bayan da aka gano yana karbar kudaden mutane da sunan zai kaiwa alkali.
Kano Focus ta ruwaito Bashir na tatsar wani Muhammad Hasasan da ake yiwa shari’a gaban Alkali Halhalatul Kuza’i da sunan alkali ne ya turoshi.
Bashir na karbar kudaden da sunan alkalin zai yi masa shari’a irin wadda ya ke so, da zai ji dadin ta amma sai ya bada lada.
Muhammad Hassan dai ya garzaya gurin mai shari’a Halhalatul Kuza’i Zakariya don jin ko shi ne ke aiko Bashir karbar kudi a hannun sa.

Sai dai mai shari’ar ya bayyana cewa ba shi da masaniya akan batun haka zalika bai san cewa Bashir na karbar kudaden mutane da sunan sa ba.
A cewar Muhammad yaga al’amarin yaki ci yaki cinyewa ne ya tafi gun alkalin bin bahasi.
Sai dai da alkali ya sa aka kirawo Bashir sai ya ce yana karbar kudaden don radin kansa ne, amma ba al’kali ke turoshi ba.
“Ya tabbatar da cewa ba alkali yake kaiwa kudin ba bayan da aka titsiye shi,” a cewar sa.
Da muka tuntubi kakakin kotunan jihar Kano Babajibo Ibrahim ya ce abinda Bashir ya aikata ya batawa mai shari’ar suna kuma cin amanar aikine.
Ya kara da cewa tuni aka mika wanda ake zargi hannun ‘yan sanda domin cigaba da gudanar da bincike tare da girbar abinda ya aikata.
Babajibo ya kuma ce tuni suka kafa kwamiti da ke bincike tare da kama masu yin sojan gona a bangaren shari’a.
Ya ce a don haka yakamata al’umma su dinga lura sosai da irin mutanen da za su yi mu’amalar shari’a dasu.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
