Connect with us

KANUN LABARAI

Ranar bandaki: Yadda matsalar bandaki ke tagayyar dalibai mata a makarantun Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

A yayin da ake bikin ranar bandaki ta duniya a yau Alhamis, dalibai mata a nan Kano sun koka kan yadda suke shan bakar azaba a makarantunsu  na rashin kyawawan bandakuna.

A kewayen da jaridar Kano Focus ta gudanar a wasu makarantun jihar nan ta gano yadda dalibai mata ke tagayyara sakamakon rashin kyawawan bandakuna.

Wasu dalibai da muka zanta da su sunce ko kadan basa iya jurewa irin kazanta da halin ko in kula da ake nunawa bandakunan makarantun nasu.

Amina Muhammad Abdulkarim daliba ce dake karatu a wata makarantar sikandiren gwamnati a nan Kano ta ce a duk lokacin da za ta shiga bandakin makarantarsu hankalinta na matukar tashi.

Ta ce a nayi musu bahaya a kan daben bandaki, da kuma gefen masai, da hakan kesa gurin ya dinga  wari.

“Makaranta bata samarda masu tsaftace bandakunan ba, domin kuwa wasu lokutanma  daliban da suka yi laifi ne suke gyara bandakunan.

“Ko idan mutum yazo a makare sai a ce washe gari yazo da Omo da abin wanke badaki, duk kuwa sanda ba a samu wani mai laifi ba to haka bandakunan za su yi ta zama ba tsafta,” inji Amina.

A nata bangaren wata dalibai mai suna Halima Nasir Ahmad dake karatu a wata makaranta mai zaman kan ta ce duk da  cewa suna da mai kula da bandakuna a makarantarsu, amma galibin lokuta bandakunan kan kasance ba gyara.

Ta ce wani lokacin gandace ke sanyawa masu kula da bandakunan basa gyarawa, da hakan ke barazana ga lafiyar dalibai.

Ko haka abin yake a manyan makarantu?

Nazarin Kano Focus ya gano suma manyan makarantun jihar nan da suka hadar da jami’a da kwalejoji ba a barsu a baya ba wajen kazantar bandaki.

Aisha Adamu dake karatu a jami’a Bayero da ke nan Kano ta ce ko kadan lamuran bandakunan makarantar sai dai addu’a.

Ta ce wani lokacinma ko ta gefen bandakunan dalibi ba zai iya wucewa ba, balle ma ya shiga don biyan bukata.

Ta kara da cewa wani lokacin sukan zabi su tafi gidajen dalibai dake cikin makaranta idan sun matsu., koma su hakura su koma gida.

“Muna kai korafi gurin hukumar makaranta amma ba safai suke sawa a gyara ba.

“Bandakunan gidajen dalibai dake cikin makaranta da kewayenta ne ma suke da dan dama-dama  da yake su suke gyarawa da kansu,” a cewar ta.

Haka zalika wata daliba dake karatu a jami’ar Yusuf Maitama Sule Maimunatu Yusuf Musa ta ce a lokuta da dama mutum ba zai iya tsayawa na mintuna biyu ba a bandakunan jami’ar saboda kazanta.

Ta kara da cewa da yawan wasu daliban idan suka shiga bandaki sukan fito suna a mai koma zazzabi saboda yanayin bandaku nan nasu.

“A kwai dalibai da dama da suka kamu da cutuka na mata da sanyi saboda kazantar dake bandakunan.

“Kuma mafi akasari daliban dake shigowa daga waje ne sukafi batawa, bana cikin makaranta ba,” inji Maimuna.

Akwai hadari mai yawa

Da yake tsokaci kan al’amarin shugaban makarantar koyar da tsaftar muhali ta jihar Kano Malam Bashir Yahya Getso ya ce mata ka iya kamuwa da cutar amai da gudawa da  ciwon sanyi saboda rashin tsaftar bandaki.

Ya ce ya zama wajibi a dinga tsaftace bandakunan dalibai domin kare su daga kamuwa da cututtukan dake da alaka da rashin tsafta.

Ko me hukuma ke?

A nasa bangaren sarkin tsaftar Kano Alhaji Jafaru Gwarzo ya ce suna sane da yadda wasu makarantun ke gaza tsaftace bandakunan dalibai.

Ya ce hakan tasa suka tura malaman tsafta a kowwace makaranta dan lura da tsaftar makarantun.

“Bamu da masaniyar makarantun da basuda bandakuna, amma matukar munsani to zamu sanarwa da ma’aikatar ilimi don a gina musu bandakuna,” a cewar sa.

Ya kuma ce tuni suka kafa kwamiti dake zagayawa makarantu don tabbatar da tsaftar bandakunan su.

Yana mai cewa matukar suka samu wata makarantar da laifin kin tsaftace bandaki to zasu hukuntata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending