KANUN LABARAI
Zaben kanan hukumomi: Fa’izu Alfindiki zai gurfana a gaban kotu
Mukhtar Yahya Usman
‘Yan takara 17 cikin 23 da suka tsaya neman shugabancin kujerar karamar hukumar birni karkshi jam’iyyar APC sun ce basu amince da tsayar da Fa’izu Alfindiki a matsayin dan takara ba.
Kano Focus ta ruwaito wannan na kunshe ne cikin wata takardar korafi kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani a karamar hukumar birin da ke dauke da sa hannun lauyan masu korafin Zainab A Mayaki.
Ta cikin takadar ‘yan takarar sunce sun zabi yin masalaha ne da aka ce musu za a tsayar da Murtala Sunusi Dawaki, amma ko kadan basu janyewa Alfindiki ba.
A cewarsu sun girmama jam’iyya da ta ce a yi masalaha, suka kuma amince atsayar da Murtala Dawaki, amma kawai sai sukaji ance ‘wai’ Fa’izu ne dan takara.

A don hakan ne suka yanke shawarar mika korafinsu ga uwar jam’iyya ta jihar Kano domin daukar matakin gyara.
Sunce matukar hakan bata samu ba daga uwar jam’iyya to basu da wata mafita illa su garzaya kotu.
Rashin can-cantar sa
‘Yan takarar 17 sunce bisa dokar jam’iyya dole ne wanda za a tsayar takara ya zama an zabenshi ta hanyar zaben fidda gwani ko kuma ayi masalaha.
A cewarsu ba su zabi Fa’izu Alfindiki ba, kuma basu yi masalaha sun janye mas aba.
Haka kuma sunce a dokar jam’iyyarsu dole ne duk wanda zai tsaya takara ya ajiye mukamin da yake kai kwanaki 30 kafin shigarsa takara.
Sai dai sunce har lokacin da aka gudanar da zaben Fa’izu Alfindiki na nan a kan mukaminsa na daya daga cikin mataimakan gwamna.
Yana da tarihin laifi
Cikin takardar da lauyar ta sanyawa hannu, masu karar sun zargi Fa’izu alfindiki da aikata miyagun laifuka.
A cewarsu an gano hoton Fa’izu alfindiki na daga allon da ke nuna ya amsa lafinsa a wani ofishin’ yan sanda.
Adon hakan ne suke cewa dukkanin wanda aka hanogo da irin wannan laifi to bai can-canci ya shugabanci al’umma ba.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
