Connect with us

KANUN LABARAI

Batanci ga Annabi: Kotun daukaka kara a Kano ta fara sauraron karar Yahya Aminu Sahariff

Published

on

Aminu Abdullahi

Kotun daukaka kara ta jihar Kano ta fara saurar karar da aka daukaka gabanta bisa hukuncin da kotun shari’ar musulunci ta yanke na kashe Yahya Aminu Sharif ta hanyar rataya bayan da aka sameshi da laifin yin batancki ga annabi Muhammad (SAW).

Kano Focus ta ruwaito mai sahari’a Nura Sagir da mai shari’a Nasiru Saminu ne suka jagoranci zaman kotun a ranar Alhamis.

Yayin zaman kotun, lauyoyin da ke kare Shariff, Barista Kola Alapini da Abdullahi Auwal Muhammad sun bukaci kotun da ta rushe hukuncin da babbar kotun shari’a tayi a baya.

A cewarsu hukuncin da aka zartaswa Yahya Aminu Sharif da Umar Faruk ya saba da kundun tsarin mulkin kasa.

Alapin ya ce lokacin da aka yi waccan shari’ar babu lauyan da ya tsayawa wadanda ake zargi, a cewarsa wannan ma ya saba da ‘yancin da suke da shi.

Ya kara da cewa karkashin sashi na talatin da takwas na kundin tsarin mulkin kasa wadanda ake zargin suna da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu, da kuma yin addinin da suka ga dama.

A don hakan ne ya bukaci kotun da ta yi watsi da wancan hukunci ta kuma salami wadanda ake zargin.

A nata bangaren lauyar gwamnati Barista Aisha Mahmud ta bukaci kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun shari’a Musuluncin ta yanke tun a baya.

A cewarta hukuncin da kotun ta yi na baya na kan tsari kuma bai saba ka’aida ba.

Da suke jawabi alkalan da suka jagoranci zaman shari’ar Nura Sagir Umar da Nasiru Saminu sun ce za su sanarwa da lauyoyin bangarorin biyu ranar da kotun za ta yanke hukuncin kan bukatar da lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar mata.

Idan za a iya tunawa dai a ranar goma ga watan Agustan da ya gabata ne  babbar kotun Shari’a dake Hausawa filin hockey karkashin mai shari’a Khadi Aliyu Muhammad Kani ta yankewa Yahya Aminu Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da tura Umar Farouk gidan gyaran hali na shekaru goma.

Hakan ya biyo bayan samun su da laifi yin batanci ga fiyayyen halitta  Annabi Muhammad S.A.W a wani videon waka da ya dinga zagaya kafar sada zumunta ta whatsapp.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending