KANUN LABARAI
Dalilai uku da suka sanya harshen turanci ke danne na Hausa
Zulaiha Danjuma
Wani masani a sashen Kimiyyar harsuna da nazarin harsunan kasashen waje a jami’ar Bayero Dakta Isa Muhammad Inuwa ya bayyana dalilai uku da ke sawa harshen hausa ke bacewa a tsakanin matasan jihar Kano da ma kasa baki daya.
Daktan ya bayyana rashin kwarewa a harshen uwa, da shigowar zamani, da kuma lalata harshen da gangan da sunan gayu a matsayin makaman da ke batar da harshen.
Malamin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Kano Focus a ranar Litinin.
Rashin iya harshen uwa
Dakta Inuwa ya ce harshen turanci ya yiwa mutane illa da dama a duniya ta yadda ya danne harshen uwa da mutane suka gada iyaye da kakanni.
Haka zalika galibin matasan Hausawa sun fi son a ce sun iya turaci fiye da harshen su na uwa da hakan ke tasiri matuka wajen tafiyar da harshen.
“Harshen turanci ya samu karbuwa a kasashe daban-daban, wajen aikin gwamnati, da harkokin cinikayya, kuma masu amfani da shi sunfi kowannen harshe a fadin duniya ta bangaren mu’amala da cinikayya.
“Yadda turanci ke yiwa harshen hausa illa haka yake yiwa wasu harsunan daban.
“Ya ce a yanzu yaro na isa shiga makaranta sai a fara turashi makaranta Nursery, saboda su koyi turanci, bayan basu gama yi kwari a nasu na uwa ba.
“Hakan ta sanya harshen turancin ke dannen na hausan a kowanne lokaci suke yin magana, saboda da shi aka fara ginosu.
Zamani
Daktan ya kara da cewa akwai abubuwa na zamani da suka shigo da kowa ma da turanci ya san su, ba kuma a fassarasu zuwa hausa, kuma matasa basa neman sanin hakan.
“Akwai abubuwa da dama da idan kace a fassara da hausa ka hada kanka da aiki, kamar ‘earpiece’ da ‘charger’ ‘recharge card’ da wasu da dama.
“To irin wadannan suna nan da yawa a cikin harshen hausa, da turancine amma an hausantar da su kuma bama a tunin sanin ma’anar su da hausan.
Lalata harshen da gan-gan
Shehin malamin ya kara da cewa matasa basa son koyar yaren da gan-gan da wasu ma a ganin su cinyewa ce a ce suna kwaba hausa saboda tsananin iya turancin su.
“Matasa yanzu da gan-gan suke bata hausar su saboda da zarar ance ka iya hausa to za a yi maka kallon na da.
“Kamar yadda za kaji wasu da sunan gayu na wasu irin kalamai na bata yaran kamar ‘wayana ne, ‘ulcer na ne’ duka wadannan lamirin mata ne da su amma sai a basu na maza da gangan.
“Haka kuma wasu abubuwan masu sauki kamar randa, tirmi sai kaji wani yana Tambaya wai meye su.
Ta ya za a inganta harshen?
Dakta ya ce iyaye na da muhimmiyar rawar da za su taka don ganin harshen hausa ya ci gaba.
“Iyaye tun a gida ya kamata sun dinga koyawa yaransu Hausa, da zarar sun ji suna fifita turanci akan harshen su.
“Kakannin su ma ya kamata su dinga zama da su suna koya musu hausa, hakan zai taimaka wajen koyon harshen.
Haka zalika likitan ya ce jin wakoki na gargajiya zai taimaka gaya wajen koyon harshen hausa, hadi ta karatun littattafai
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.