KANUN LABARAI
Ranar yaki da kanjamau: Hisbah ta kama masu yada kanjamau sama da 40 a Kano
Aminu Abdulahi
A ya yin da ake bikin ranar yaki cutar kanjamau ta duniya a yau Talata, hukumar Hisbah ta kama maza ta mata kimanin arba’in masu dauke da cutar Kanjamau kuma suke yada da ga sauran jama’a a Kano.
Kano Focus ta rawaito hukumar ta kama mutanenne a kasuwar saida kayan gwari ta Badume dake karamar hukumar Bichi.
Kwamandan Hisbah na jihar Kano Muhammad Harun Ibn Sina ya ce sun kama mata guda talatin da biyu sai kuma maza guda goma.
Ya kara da cewa bayan da aka kama su ne suna yawon ta zubar, sai aka yi musu gwaji, inda bincike ya nuna cewa mutum goma sha biyu daga cikin matan na dauke da cutar ta kanjamau.

Ya ce mutum bakwai daga cikin matan sun san suna dauke da cutar ya yin da kuma ragowar matan suka fahimci hakanne bayan sakamakon gwajin da akayi musu ya fito.
KORONA: Hisbah ta fara binciken kwamandan da ake zargi da sace kayan tallafi
Masarautar Rano ta dakadar da dagatai biyu da suka sace tallafin Korona
Hisbah ta dakatar da kwamandan da ake zarigi da sace tallafin Korona
Bayan da aka bayyana musu hakane sai kuma suka barke da kuka sakamakon rashin sanin cewa suna da ita.
Ya kuma ce wasu daga cikin wadanda aka kama din ba ‘yan jihar Kano ba ne, sun zo ne daga makwaftan jihohi.
Majalisar dinkin duniya dai ta ware ranar daya ga watan Disambar kowace shekara a matsayin ranar cutar kanjamau ta duniya don nuna goyan baya ga mutanen dake dauke da cutar da kuma tuna wadanda suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar cutar ta kanjamau.
A cewar Hukumar lafiya ta duniya mutan miliyan 38 ne ke dauke da cutar ta kanjamau a fadin duniya.
Haka kuma fiye da kaso sittin na wadannan mutane sun fito ne daga najiyar afrika.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
