Connect with us

KANUN LABARAI

EFCC ta cafke tsohon shugaban kasuwar Kofar Wambai a harabar kotu

Published

on

Aminu Abdullahi

Hukumar (EFCC) ta cafke  tsohon shugaban kungiyar kasuwar kofar Wambai Musa Sani Mainagge jim kadan bayan fitowarsa daga kotu lokacin da ake sauraron shari’arsa.

Kano Focus ta ruwaito hukumar ta EFCC ta cafkeshi ne a harabar babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Laraba.

Idan za a iya tunawa, an gurfanar da wanda ake zarginne a gaban babbar kotun tarayya mai lamba biyu karkashin mai shari’a A.A Oguwatu bisa zargin sa da karkatar da kudaden wasu mutane da ya karba da zummar sayar musu da rumfuna a kasuwar Kantin kwari.

A na dai tuhumar tsohon shugaban da karbarwa Abdullahi Uba N5,000,000 sai kuma Dauda Abubakar da ya karbar masa N3,700,000 yayin da ya karbi N5,000,000 daga hannun Alhaji Rabi’u.

Batanci ga Annabi: Kotun daukaka kara a Kano ta fara sauraron karar Yahya Aminu Sahariff

Zaben kanan hukumomi: Fa’izu Alfindiki zai gurfana a gaban kotu

Rashawa: An kama ma’aikacin kotu da ke karbar kudade da sunan al’kali a Kano

Sai Auwalu Ibrahim da Malam Musa Sani Mainaggen da ya karbarwa N9,000,000 sai kuma Mahmud Mukhtar  da kuma Mudansir Ahmad da ya karbar musu N650,000.

Haka zalika ya sake karbarwa wani mai suna Alhaji Magaji N5,000,000  duk da sunan zai samar musu da rumfuna a kasuwar Kantin kwari.

Sai dai bayan mai shari’a ya dage zaman sauraron karar bayan da ya saurari shaidun da aka gabatar zuwa ranar 26 ga Disambar 2020.

 

Haka kuma bayan ya fito ne daga kotun jami’an Hukumar ta EFCC suka sake cafkeshi a harabar kotun bisa wasu sabbin zarge-zargen

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Trending