KANUN LABARAI
Zaben kananan hukumomi: PDP a Kano ta kaddamar da asusun neman taimako
Mukhtar Yahya Usman
Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta kaddamar da asusun neman taimakon sama da naira miliyan dari, domin samun damar tallafawa ‘yan takararta da za a fafata da su a zaben kananan hukumomin da ke tafe.
Kano Focus ta ruwaito jam’iyyar ta PDP ta kaddamar da asusun ne ya yin taron da ta gabatar ranar Lahadi a gidan tsohon minstan tarayya Ambassador Aminu Wali.
Idan za a iya tunwa, a baya ne tsagin Kwankwasiyya a jam’iyyar ta PDP ya ce ba za su shiga zaben ba saboda suna hago rashin adalici da magudi da aka shirya tafkawa.
Sai dai tsagin na Aminu Wali ya sanar da cewa ba da yawunsu aka yi wancan zance ba inda ya ce su kan za su shiga a dama da su.

Da yake jawabi a madadin ‘ya ‘yan jam’iyyar, mai rikon mukamin shugaban cin jam’iyyar a nan Kano Muhammaina Bako Lamido ya ce manufar kafa asusun shi ne domin a tara kudaden da za a tallafi ‘yan takar da za su tsayawa jam’iyyar ta PDP.
Ya ce idan an tara kudaden da su ne za a siyawa ‘yan takarar takardar shaidar tsayawa takar, a kuma tallafi yakin neman zabe su.
Ya ce jam’iyyar PDP a idon uwar jam’iyya ta kasa bata da wani katabus, hakan ce ta sanya za su nuna musu cewar har yanzu ruwa na maganin dauda.
PDP a Kano ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi ba
Baku da inuwar da za ku tsaya takara ne- Martanin gwamnatin Kano ga Kwankwasiyya
Ko jam’iyyu a Kano za su baiwa matasa dama a zabukan da ke tafe
“Ina kiran dukkanin ‘yan takarar da aka tsayar a daukacin kananan hukumomin jihar nan 44 da sufara yakin neman zabe.
“Muna so uwar jam’yya ta kasa da sauran abokan hamayyarmu su san muna nan a Kano.
“Mun yanke shawarar kafa wannan asusun ne domin mu baiwa kanmu damar daukar nauyin ‘yan takararmu da kuma yakin neman zabensu a fadin jihar nan.
“Muna da kyakyawa fatan cewa zamu yi nasara a zaben da za a gudanar, ba kamar yadda daya tsagin ya karaya ba, muna da kyakyawan fatan hukumar zabe da za ta yi mana adalci kan lamari.” A cewar sa.
Da ya ke nasa jawabin guda daga cikin shugabancin jam’iyyar tsagin Aminu Wali Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya bukaci dukkanin ‘ya ‘yan jam’iyyar da su fito kwansu da kwarkwata ranar zabe su zabi jam’iyyar ta PDP.
Ya kuma ja kunnen hukumar zabe ta jihar Kano KANSIEC kan magudun zabe, a cewar sa ba za su lamunci dukkanin wani magudi ba.
Gwarozo wanda ya bata tallafin miliyan biyar ya ce jam’iyyar su na da karfi sosai da za ta kara da jam’iyyar APC kuma ta yi Nasara.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
