Connect with us

KANUN LABARAI

Bama tsoron barazanar Abdullahi Abbas- PDP

Published

on

Aminu Abdullahi

Jam’iyar PDP a jihar Kano tace ta shirya tsaf don tunkara duk wata barazana da jam’iyyar APC ko mabiyanta za ta zoma ta da shi.

Kano Focus ta ruwaito shugaban jam’iyar na jihar Kano Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Wada Sagagi ya ce hankalinsu ya kai kan wani bidiyo  da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani da aka nuno mukaddashi jam’iyyar APC a Kano Abdullahi Abbas na yin wasu kalamai na tada tarzoma a cikin jama’a.

Idan za a iya tunawa dai a farkon makona nanne aka jiyo Abdullahi Abbas na wasu kalamai da ka iya tada hargizi ko jawo tarzoma a cikin jama’a.

Abdullahi Abbas ya ce “Zamanin zabe na gaskiya da adalci ya kare a Kano.

“Za mu tabbatar da maimaita zabenda bai kammala ba (inconclusive) a kakar zaben mai zuwa ta 2023.

“APC za ta ci gaba da mulki tun daga kasa har zuwa tushe.

“Ba za mu bari ayi zabe mai kyau ba, kuma za mu sake maimaita irin  zaben 2019 da bai kammalu ba, za mu murde zaben kamar Gama.

“Ina kira gareku da karku tausaya wa duk wani mai kishin Kwankwasiyya”, a cewarsa.

Ba ma maida hanka kan irin wadannan kalaman

Sai dai Shehu Wada ya ce a mifiya yawan lokuta basu fiye ba da muhimmanci ga irin wadannan kalamai ba musamman ga abinda Abdullahi Abbas ya sabayi na yin kira ga tashin hankali da kowa ya san shi akan hakan.

Ya ce da farko sunyi shiru, amma saboda mauhimmancin da ke cikin batun da ya furta, da kuma la’akari da ‘yan baya ya zama wajibi su saita al amura.

Ya kara da cewa bayyanar kalaman batanci da hargitsi da fitina a fili ya sake bayyanawa mutane cewa APC ba ta wakiltar duk wata manufa ta dimokiradiyya.

“Hakan ya nuna wa jama’a jam’iyyar keda alhakin  duk kan tashin hankali dake faruwa waɗanda dama mun riga mun san cewa suna da laifi.

“Mafi muhimmanci shi ne ya bayyana shirinsu na nan gaba wanda ke nuna cewa za su karbi mulki ta kowacce hanyar tashin hankali,” a cewar sa.

Ta tabbata murde zabe APC ta yi

Ya ce duba da abinda ya gabata da  maganganun Abdullahi Abbas, yanzu ana iya la’akari da wadanan  abubuwa a matsayin gaskiya.

“Zaben gwamna na 2019 tsari ne na demokradiyya da  Abba Kabir Yusuf ya yi nasara amma aka murdeshi ta hanyar haramtaccen tsari wanda ake kira INCONCLUSIVE.

“Rikicin da ya faru a zagaye na biyu na zaben an shirya shi ne kuma APC ce ta aikata.

“Manufar APC a zabe mai zuwa na 2023 ita ce ta sake nuna irin tashin hankalin da ta nuna a 2019 ba don shiga cikin tsarin demokradiyya a lumana ba,” inji Sagagi.

“Don haka muna kira ga mutanen kirki na jihar Kano musamman mambobin PDP da su kasance masu jajircewa, da bin doka da kuma bijirewa duk wani nau’i na tsoratarwa daga jam’iyya mai mulki.

Jami’an tsaro su sanya idanu

Ya kuma yi kira ga Kwamishinan ‘yan sanda da shugaban hukumar tsaro na farin kaya na jihar Kano da duk sauran jami’an tsaro da su lura da kuma rubuta matsalolin da maganganun da aka fada za su haifar.

Haka zalika ya yi kira ga bangaren shari’a, da kwamishinan zabe na Jihar Kano, da ya yi la’akari da bayanan gaskiya na zaben gwamna na shekarar 2019 da kuma shirinsu na yin magudi a babban zabe na 2023 wanda PDP a matsayin jam’iyya za ta yi tirjiya sosai

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending