Connect with us

KANUN LABARAI

Zargin badakalar Tracker: Kotu ta ce a biya Bappa Babba N50,000 ladan bata masa lokaci

Published

on

Aminu Abdullahi

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller Road ta yi umarnin da a biya shugaban hukumar KAROTA Bappa Babba Dan Agundi N50,000 ladan bataba masa lokaci.

Kano Focus ta ruwaito wannan na zuwa ne jim kadan bayan da ta yi watsi da bukatar da kotun majistire tayi na neman Bappa Babba da ya bayyana a gaban ta kan zarigi badakalar Tracker.

Kotun karkashin mai shari’a Usman Na’abba ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin.

I dan za a iya tunawa dai kotun majistire dake gidan Murtala ce ta bada umarnin shugaban hukumar taKAROTA da ya bayyana a gabanta.

Hakan ya biyo bayan korafin da wani direban Adaidaita Sahu ya shigar yana kalubalantar hukumar KAROTA da shugaban hukumar bisa bashi takarda a matsayin tracker bayan da ya biya kudi.

Mai karar ya bayyanawa kotu cewa hukumar KAROTA ta umarci masu baburan Adai-daita sahu da su mallaki na’urar don magance aikata miyagun laifuka a jihar Kano ta hanyar amfani da baburan Adaidaita Sahu.

Hukumar KAROTA za ta tara harajin sama da miliyan dubu a shekar 2021

Tunda an yafe mana a sakar mana kudadenmu-dakatattun ‘yan majalisar Kano

Hukumar KAROTA za ta tara harajin sama da miliyan dubu a shekar 2021

Ya ce bayan da suka biya kudinne kuma sai hukumar ta basu takarda a maimakon na’urar .

A cewarsa hakan ce ta sanya suka kai kara gaban kotun domin bin hakkin su

Sai dai kuma hukumar KAROTA ta garzaya babbar kotun jiha domin kalubalantar hukuncin kotun majistiren.

Bayan sauraron kararne, sai mai shari’a Usman Na’abba ya sallame ta tare da cewa kotun majistiren bata da hurumin sauraron karar.

Haka zalika mai shari’ar ya kuma nemi mai karar da ya biya Baffa Babba Dan Agundi naira 50,000 bisa bata masa lokaci da kuma biyan sa duk kan kudaden da yakashe a kotu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Trending