KANUN LABARAI
Shin ya kamata a fara siyarwa da jama’a wurin da za su binne matattunsu
Aminu Abdullahi
Biyo bayan karancin da ake samu na wuraren binnen mutane a makabartun da ke jihar nan al’umma na kiraye-kiraye mayarda makabartu tsarin kasuwanci.
A zantawar Kano Focus da wasu daga cikin jama’ar Kano, sun ce ana samun karancin mawadatan da ke iya siyan filaye su kuma bayar sadaka domin a dinga binne jama’a.
Hakan ta sanya da wuya a je binnen mutuma a makabarta a tarar wurin da za a binne shi ba wuri ne da aka taba binne wani ba.
Hakan ta sanya masu kiraye-kirayen ke cewa ya kamata a fara yanka fili na siyarwa domin binne mutane.

Haka zalika bincike ya nuna cewa ba safai gwamnatin ke samar da filaye domin yin makabartu ba.
Idan gwamnatin ta samar a wasu lokutan za a iske dillalai sun sayar.
Abiya dubu goma don binne mamaci
Mukhtar Muhammad Adam mazaunin unguwar Dorayi ne, ya ce kamata ya yi mawadata su rinka siyan fili suna daukar ma’aikata da za su kula da shi ta yadda duk wanda ya zo binne mamaci zai biya kudi.
Ya ce idan har a ka samu wadanda za su rinka siyan fili su gina famfon tuka tuka da biyan ma’aikata to hakan zai sa a dena samun matsalar karancin makabartu da ake fuskan ta a jihar.
“A kalla a ce naira dubu goma za a biya ga kowane mutum da za a binne inaga hakan zai rage matsalar rashin aikin yi da ake fama dashi.
“Idan wani ya yi aka ga ana samun kudi to da yawan mutane za su rinka siyan filaye kuma za a samu yawaitar makabartun,” a cewar sa.
Aliyu Muhammad Ali dake unguwar gidan Zoo cewa ya yi matsala ce babba yadda ake samun makabartu na cika, ba kuma tare da samun sababbi ba.
Ya ce abin takaici ne yadda a yanzu ake samun karancin masu bada makabarta sadaka a cikin al’umma.
Ya kara da cewa tun da dai ana cikin matsalar tsadar rayuwa ta yadda wasu ke kyashin bayar da kyauta to maida tsarin kasuwanci shine mafita.
Sayar da fili dan binne mamata matsala ne
Murtala Mustapha mazaunin hotoro ya ce ana yawan mace -mace kuma makabartun da ake da su sunyi kadan duba da yawan al’ummar jihar Kano.
Ya kara da cewa da yawan gina masallatai da mawadata ke yi kamata ya yi su maida hankali wajen Samar da makabartu duba da cewa masalllatan da ake dasu sunyi yawa.
“Ni bana goyan bayan maida makabartu harkar kasuwanci ,don hakan ba tsari bane kuma mu musulmai an sammu da sadaukar wa.
“A kwai matsala babba matukar aka wayi gari a jihar nan akace sai mutum ya biya kudi zai binne dan uwan sa,” a cewar sa.
Muhammad Dauda a unguwar Hotoro cewa ya yi laifin gwamnati ne na rashin tilastawa masu fitar da filaye a sabbin unguwanni samar da makabarta.
“Mutum ne zai yanka filoti fiye da tamanin ko dari amma ba zai yi adalci ya fitar da filin makabarta ba sai yaga dama ma zai fitar da dan karamin guri a matsayin masallaci.
“Kamatà ya yi gwamnati ta rinka bi duk inda ake fitar da sabbin gurare a ce ana fitar da makabartu,” a cewar sa.
Ke meneni ra’ayin malamai?
Wani malamin addinin musulunci mai suna Ibrahim Siraj Adhama ya ce tun asali al’umma ke samarwa kansu makabartu a cikin birane.
Ya kara da cewa matsalar karancin makabartun tafi yawa ne a cikin birni ba kamar kauyuka ba da mafi akasari suke binne ‘yan uwansu da suka rasu a bayan gidajen su ko wani bangare na gidajen nasu kuma mafi yawa gonakin sune.
Ya ce akwai manyan makabartu a jihar Kano da za su wadaci al’ummar da ake dasu matukar za a gyara tsarin yadda ake binne mamata.
“Makabartar Bakiya dake kusa da masallacin Annabi S.A.W a Madani ana binne mutane a ciki tun Ma’aiki S.A.W yana raye gashi har yanzu.
“Saboda tsarin da suke amfani dashi ba irin namu bane ba a baiwa mamaci gurin zama na dindin din.
“Idan ka cire Sahabbai da sauran manyan mutane duk wanda aka binne ya samu shekaru fatar ta zama kasa sauran kasusuwan tattare su akeyi sai ayi rami daga gefe a binne.
“Gurin kuma sai a sake binne wasu mutanen a ciki amma mu makabartun mu basu kai wadan nan shekarun ba amma ana cewa sun cika,” a cewar sa.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
