Connect with us

KANUN LABARAI

Auren Janine da Sulaiman ya bar baya da kura a Kano

Published

on

Zulaiha Dajuma

Tun bayan da aka daura auren Sulaiman Isa da Janine Sanchez a ranar Lahadin da ta gabata, al’umma a Kano ke ta tofa albarkacin bakinsu.

A zantawar jaridar Kano Focus da wasu matasa a nan Kano sun ce burin da mata ke da shi ne ya sanya ake haurowa har gida ana dauke musu mazajensu.

Ya yin da  wasu kuma sukace  kwadayin mazanne da neman biyan wata bukata ya sanya suke makalewa matan turawan, ya yin da wasu kuma saka ce hadi ne kawai daga Allah.

A soke lefe ko mu daina auren na gida

Wani matashi Abubakar Adamu Damisa ya ce yanzu lokaci ya yi da yakamata mata su cire buri da kwadayi su fuskanci abinda ya ke dai-dai.

“Ni a matsayina na saurayi zan iya cewa abune da muke farin ciki da shi, kuma Allah ya kawo irin su, suyi ta dauke samarin tunda su matanmu na nan burikan su sun fiye yawa”

“Turawa ba ruwansu da lefe da sauran abubuan da suka rufewa mata ido.

“Yanzu sai dai kawai a zo a dau ango ba kamar yadda aka saba gani ana daukan amarya ba.

“Idan matanmu basu dawo sunyi karatun ta nustuba, to tabbas za a fara ci gaba da duko turawa ana kyalesu gaba daya.

To sai dai a cewar wani matashi kuma dan gwagarmaya Aliyu Samb,  auren Sulaiman wani al’amari ne da ya zo da sabon salo.

Ya ce  auren ya nuna yadda zumunci ya ke da kuma damar auratayya a tsakanin muslmi da kuma ahlil kitabi.

“Ita baturiya, shi kuma dan Najeriya, akwai banbanci mutuka a tsakanin su ya zamanto kamar kulla zumunci ne.

“Irin wanna ake fata duniya ta samu, domin zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin kabilu mabanbanta da kuma addinai.

Ba zamu watsar da matan gida ba

Aliyu Samba ya kuma yi watsi da kalaman da ke cewa, mazan Kano za su watsar da matan gida domin su koma auren turawa.

Ya ce ai ba namijin da yake tsallake matar da Allah ya rubuta masa.

Idan baturiya aka rubuto masa to zai aura, idan kuma tamu ta gida aka rubuto masa to komai kwadayin sa da waccan din sai dai ya kalla daga nesa.

“Kaddarar mutune ke tabbata, ba auran matan turai ne zai sa matan mu na gida su kasa auruwa ba, haka auren mu na gida ba shi ne zai sa turawa su ki auruwa ba.

“Mazan turai za su iya zuwa nan su auri mata bakake, anyi, kuma anayi, mazan mu za su iya auran matansu matanmu za su iya auran mazajen su ba laifi bane” A cewar sa.

Kwadayi ne ya kaishi auren baturiya

Ita kuwa wata budurwa anan Kano Amina Adam ta ce, ita dai a fahintar ta kwadayi ne da son cimma wata manufa ya sanya Sulaiman Auren Janine.

Ta ce ta zauna a kasar turawa ta kuma ga yadda suke gudanar da rayuwar soyyayar su, a cewar ta ba ko sahakka lamarin su ba soyayya ba ce, illa nufin cimma wani buri.

“ Ban taba ganin wanan a matsayin soyayya ba, duk da dai jama’a na cewa soyayya ce.

“A matsayina na wadda ta taba zama a turai, duk da dai na san shi bai taba zama kasar turai ba, na ga irin wadannan  aururrukan.

Ana amfani da turawane domin a cimma wani burin na rayuwa, ciki kuwa har da neman takardar zama a turai.

Ta kuma ce dukkanin wanda ke ganin auren Sulaiman ya budewa maza Kofar auren turawa to shakka ba bu yana cikin hadari mai yawa, domin ba zai fahinci al’amarin ba har sai ya shiga cikn sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending