Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yar gwagwarmaya Zainab Nasir ta mayar da martani kan kalaman ‘Aure ba nasara bane’

Published

on

Zulaiha Danjuma

Zainab Nasir fitacciyar yar gwagwarmayar nan a nan Kano ta mayar da martani kan suka da jama’a ke  yi mata a shafukan sada zumunta biyo bayan ganinta da aka yi a bikin Sulaiamn da Janine.

Idan za a iya tunawa, Zainab Nasir ta shiga tsaka mai wuya ne bayan da ta yi wani furuci a shafinta na Facebook da ya ke cewa yin aure ba nasara ba ne’.

Lamarin dai ya jawo mata zagi da tsinuwa daga bakin jama’a da dama a jihar nan.

To sai dai ‘yar gwagwarmanyar ta ce kawai ana so a munanan mata za to ne, ya sanya aka dauki maganarta ba dai-dai ba aka kuma yadata da gangan dan a jawo mata zagi.

An dai gano Zainab Nasir ne cikin wasu hotunan bikin Sulaiman da aka wallafa tana  walwala a lokacin da ake tsaka da shan biki.

Hakanne ya sanya jama’a da dama suka dinga aike mata da martani da kuma rubutu a shafukan sada zamunta na cewar ita da ba ta dauki aure da muhimmanci ba me kuma ya kaita walwala da jin dadi a auren wasu.

Hamisu Doguwa na daga cikin wadanda suka mayar mata da martini inda ya rubuta a shafinsa na Facebook tsohuwar budurwarsa ce ta halrci daurin auren.

Shi ma wani Kabiru Isa ya ce “wacce ta ce aure ba Nasara bane kun ganta ta halarci dauren auren wasu tana murna”

Ba a yi min adalci ba

Sai dai a zantawar ta da jaridar Kano Focus Zainab Nasir ta ce abin ya bata mamaki yadda jama’a suka bar batun auren suka koma chaccakarta kuma sam ba a yi mata adalci ba.

“Mutane a social media ba za su yi magana a kan abun daya dace ba sai akan abun da bai ma cancanci ayi magana ba.

“Yanzu a halin da Arewa ke ciki muna da abubuwa da dama da ya kamata a dinga fada, kamar rashin tsaro da sace sacen yaran makarantu da ake yi amma ba za a fada ba sai wani abu can marar amfani.

“Abun bai ban haushi ba kuma bai batamin rai ba, sai dai abun ya ban mamaki” A cewar ta

Zainab ta kuma mayar da martanin kan zarigin da ake yi mata na cewa ta soki aure.

“Yawancin mutane ko kadan basu fahinci rubutun da nayi a baya ba ballanta su fahici sakon da ya ke ciki.

“In zan iya tunawa nayi rubutun a watan Mayun shekarar 2019, sama da shekara daya kenan da ‘yan watanni.

Lokacin da na yi wannan rubutun manufata shi ne nayi magana akan yadda ake tsangwamar mata da basu da aure a cikin al’umma.

“Ana ganin duk wani iliminsu, basirarsu ko wani abu na girma da suka samu bashi da wata daraja.

“ Yadda mata ke shan wahala a hannun wasu mazajen, na tauye musu hakkinsu ne ya sanya na ce yin aure a wurin airin wadannan matan ba Nasara bane.

Mace na yin auren don ta huta ta kuma samu ci gaban rayuwa, amma sai jama’a suka datse rubutun sama da na kasan suka fito da iya kalmar auren ba Nasara bane.

“Wannan shi ne tsantsar rashin adalci a ganina, da an fuskanci lamarin da ba a zarge ni ba.

“Nayi kira ne ga wanda suke tsangwamar mata wanda basu da aure a kan cewa su dena”  A cewar ta.

Sai dai ta ce ko kadan bata yi nadamar abinda ta rubuta ba tun da ida ita ba aure ta soka ba wahalar da ke cikin auren ta soka.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending