Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan daba sun kone gida jami’in Vigilante tare sassara kwamadansu a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kone gidan wani jami’in kungiyar Vigilante mai suna Malam Magaji da ke unguwar Dawanau Sabuwar Abuja a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kano focus ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan da ‘yan vigilante na unguwar suka kama daya daga cikin ‘yan daban tare da mika shi hannun ‘yan sanda.

‘Yan daban dai sunje wajen da akeyin mauludine suka tayar da hatsaniya, lamarin da yasa jami’an kungiyar suka kai musu sumame tare da kwace miyagun kwayoyi.

Daga bisani ‘yan daban suka farmaki ‘yan vigilante, inda suka kone gidan mataimakin  shugaban kungiyar tare da sassara  kwamandan su mai suna Babangida Abubakar.

Babangida Abubakar ya ce yana zaune ne akan mashin sai kawai yaji an rufe shi da sara inda suka sareshi har guri uku a jikin sa.

Yadda muke komawa alarammomi domin mu damfari jama’a a Kano

An tsinci gawar yaro dan shekara 4 yashe cikin mota a Kano

Ina hada baki ne da ‘yan unguwa su gayamin wanda ke da kayan da za a sata-Barawo

“A ranar Lahadi mun kai musu sumame, har muka kama tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi, kuma mun kama wasu daga cikin su.

“Ina zaune kuma sai suma suka zo suka hauni da sara, suka sareni a hannu da kafafu na wasu kuma suka je suka kona gidan mataimakina,” a cewar sa.

Ya kara da cewa tuni aka kama wasu daga cikin ‘yan daban da ake zargi da aikata laifukan kuma an mikasu hannun hukumar ‘yan sanda.

Ko a makon da yagabata ma sai da wasu matasa da ake zargin ‘yan dabane suka kone ofishoshin kungiyar ‘yan vigilante dake unguwar Rijiyar Lemo.

Shugaban kungiyar ‘yan vigilante dake jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji ya bayyanawa Kano Focus cewa ‘yan daban sun kone ofisoshin ne a Dan Rimi Transformer dake unguwar Rijiyar Lemo.

Da kuma ofishin su dake Dan Rimi Boda biyo bayan kama wasu daga cikin su da kungiyar tayi.

Haka zalika ya ce sun kone gurin da daya daga cikin kwamandan kungiyar yake gudanar da sanar sa ta sayarda shayi mai suna Ilulu Muhammad.

Muhammad Kabir Alhaji ya kuma ce kungiyar tasu Kano na fama da karancin kayan aiki wanda hakan ke kawo musu tasgaro kan yadda suke gudanar da ayyukan su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending