KANUN LABARAI
Jaura za ta wuce ranar 30 ga Disamba a Kano
Mukhtar Yahya Usman
Hasashen masana yanayi ya bayyana cewa a daren ranar 30 ga watan Disambar da muke ciki a ke sa ran jaura za ta wuce a Kano.
Kano Focus ta ruwaito jadawalin hasashen yanayi na accuweather ya nuna cewa a ranar 30 ga watan yanayin sanyi a Kano zai kasance mai tsanani a matakin digiri 6 kacal.
Haka zalika tun daga ranar 18 ga watan da muke ciki sanyi zai ci gaba da karuwa a cikin dare.
Hasashen ya nuna Kano a daren yau Juma’a yanayin zai kasance a matakin digiri na 13 kan ma’aunin salshiyos.

Haka zalika a ranar 19 da 20 da kuma 21 yanayin sanyi zai karu zuwa digiri 12 kan ma’auni salshiyos
Sai dai hasashen ya ce za a samu dan sauki kadan a daren ranar 22, inda yanayin zai kasance kan digiri 13, sannan washe gari ya sake kunno kai kan ma’auni salacious 11.
Haka kuma a daren ranar 24 ana sa ran sanyi zai kara tsananta akan digiri 9 kan ma’aunin salshiyos.
Sanyi zai sake kunno kai ba kakkautawa a daren ranar 24, da 26 da 27 inda zai kasance a kan digir bakwai kan ma’aunin salshiyos.
Zai kuma dan ja baya kadan a daren ranekun 28 da 29, kan diri 8 a ma’aunin salacious.
Haka zalika hasashen ya nuna cewa daren ranar 30 ga Disamba shi ne daren da za yi muku mukun sanyin da ya fi na kowacce rana a wannan shekara akan digiri 6 a ma’aunin salacious.
Dadaga nan ne kuma zai fara ja da baya a hankali a hankali har ya fice baki daya cikin abin da ba gaza wata guda da rabi ba.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
