KANUN LABARAI
Dalilai biyar da ke sa mata mantawa da Allah lokacin biki
Zulaiha Danjuma
Galibin mata na shiga wani yanayi na mantawa da ibada lokacin shagulgulan biki, da har ta kan kai su mance da yin salla tsahon wuni guda.
Wani bincike da jaridar Kano Focus ta gudanar ta gano yadda galibin matan ke kin yin sallar saboda dalilan kwalliya, da yanayin hidimar bikin.
Sauran dalilan su ne yanayin kayan da matan ke sawa masu kama da tsirara, sai kuma hayaniyar wurin biki, da kuma uwa uba rashin son kada abu ya wuce su ba a yi da su ba.
Kwalliya (make-up)

Wata matashiya Hauwa Ibrahim da jaridar Kano Focus ta zanta da ita, ta ce kwalliya ita ce abu na farko da galibin ‘yan matan ke sanyawa su kauracewa yin salla.
“Make-up yana cinkin abun da ke hana mata yin sallah a wurin biki saboda in akayi kwalliya ba a so a wanke ta” A cewar ta.
Nusaiba Magaji ita kuma cewa ta yi mata da yawa sun gwammace sallar ta wuce su da dai su wanke kwalliyar da ke fuskarsu.
“Make-up ne ke hana yawancin mata yin Sallah lokacin biki, wasu matan tun karfe 4 suke zuwa a yi masu kwalliya duk da cewa bikin ma sai 7 ko takwas za a fara.
“Ba zai yiwu ka bata irin wanna kudin da kuma lokacin ka ba, kuma a ce ka wanke lokaci kankani, kawai ya fi sauki mutum ya hade sallar ba ki daya kawai.” A cewar ta
Hidimar Biki
Ita kuwa wata budurwa mai suna Amira Sani ta ce wani lokaci kai
ne ke dukan zafi musamman ma idan al’amuran bikin suka yi yawa.
“Wasu mata zirga-zirgar da suke yi dan tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata ne ke sanya su mantawa da sallah
“Ko da ya ke hakan ba dalili bane, amma za ki ga wasu basa samun zama ne, saboda kujiba-kujiba” A cewar ta.
Matsewar kayan biki
Haka zalika wasu matan sun alakanta kaucewa yin ibadar da irin kayan da matan ke sawa da ko kadan ba za su basu damar yin sallar ba.
Amira Sani ta ce wani sa’in irin kayan da matan ke sanyawa basa kallon gabas ko kadan.
“Wasu matan hannun rigunansu ba dogo ba ne, ko kuma kayan ya matse, da ba zai yi sallah ba”.
“Wani lokacin kuma hannun kayan dogo ne amma ya matse ba zai bari a iya wanke hannu ba in za’ayi alwala.
“Ida za yi sallah dole sai dai a cire rigar baki daya, kuma samun wurin cirewar shima garari ne.” ta ce.
Hayaniyar wurin
Haka zalika dalili na gaba shi ne rashin samun wurin da babu kade-kade a lokacin bikin, shima na daya daga cikin abun da ke hana mata sallah.
Hauwa Sani wata budurwa ce a nan Kano da itama ta bayyana nata dalilan.
“Wata cewa za ta yi gurin sallah ne babu saboda cikin hall din ba wurin da za ta iya rakabewa tayi ba tare da hayaniya ba”
Haka zalika Farida Abubakar ta ce samun wuri mai nutsuwa abune mai wahala da biki, amma hakan bai zamewa mata hujjar kin yin sallah ba.
“In kin dauki Sallah da muhimmanci za ki samu yadda za ki yi duk hayaniyar wurin, duk da dai nasan yawanci wuraren biki babu wurin sallah” A cewar ta
Son ganin kwakwaf
Su kuma wasu matan sun ce rashin son kar a basu labarin yadda amarya ta shigo wurin biki ko yadda wani mawaki ya raira waka, kan sa su mancewa da ibada.
Hauwa Ibrahim ta ce wata in ta zo biki tanaso a ce anyi komai a kan idanuwanta, ko dan motsawa ba ta son yi dan ita a ganinta wani abu zai wuceta”
“Dan haka wata sai ta ajiye sallar dan gudun kar’ayi ba ita, sannan ta zabi hade sallolin idan ta koma gida.
Mahangar addini
Sai dai Kano Focus ta tuntubi babban malamin nan na Kano, Malam Abdallah Gadon Kaya, inda ya ce kwalliya ba laifi ba ne lokacin biki, sai dai kin yin sallah saboda kwalliya haramunne.
Ya ce mace za ta iya kwalliya idan ‘yan uwanta matane za su ganta, amma duk macen da saboda kwalliya ta kauracewa yin salla to ta saurari gamuwarta da Allah.
“Duk wacce tayi kwalliyar da ta san ba za ta yi sallah ba tana cikin fushin Allah”
“Babu babban fushi da ya fi mutun ya ki yin sallah, kuma wannan bikin Allah ba zai musa Albarka ba, kuma masu bikin ba lallaine Allah ya yi musu albarka ba, saboda an tozarta Allah, an tozarta shari’a Allah.
“Ibadar da ta fi kowacce muhimmanci an wulakantata a wannan bikin” A cewar sa.
Shawara
Malamin ya ba da shawarwari na kiyayewa da kuma samun yin sallah a yanayin biki.
“Idan makeup zai hana a yi sallah to a hakura da shi, ko ayi a wanke shi, idan lokacin sallah ya yi sai a koma ayi wani, a nuna cewa sallah ta fi make-up daraja, a wanke shi”
“In ba haka ba, ayi alwala sannan a yi kwalliyar a rike alwala, idan lokacin sallah ya yi ayi sallah ba sai an maimaita alwala ba” A cewarsa.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
