Connect with us

KANUN LABARAI

Hukumar NIMC ta samar da hanya mafi sauki domin rijistar katin dan kasa

Published

on

Hukumar dake samar da katin shaidar dan kasa (NIMC) ta fitar da fom ga wadanda ba su samu damar mallakar katinba domin yin rijista cikin sauki ba tare da zuwa ofishin hukumar ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa hukumar ta sanar da fitar da fom dinne a shafinta na facebook a ranar Lahadi domin saukakawa masu yin rijista bin layi.

Sanarwa ta ce al’umma za su sauke fom din ne a takarda a gurin masu kwamfuta, sanna su cike bayanan da aka nema.

Da zarar an kammala cikewa kuma sai a ɗauke shi  zuwa ofishi ko cibiyar da ake yin shaidar katin ɗan kasa.

Haka zalika sanarwar ta ce dole ne duk wanda zai kai fom din ya tafi da shaida cewa shi dan asalin jihar sa ne da kuma takardar haihuwa da lambar waya mai aiki.

Haka zalika hukumar ta gargadi al’umma da su kaucewa ‘yan damfara da ka iya kiran su da sunan hukumar samar da katin shaidar dan kasa ko kamfanonin layukan waya.

Ta ce irin wadan nan yan damfarar ba za su tambayi lambar BVN ko ta NIN ba maimakon haka za su tambayi da abasu NIN Verification Code wanda kuma hanyace da za ta basu damar yin swaping na laying mutum da kwashe kudin asusun sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Hausa

Shugabannin Fulani sun goyi bayan takarar Tinubu

Published

on

Aminu Abdullahi

 

 

Shugabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.

A taron da suka yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawarin yin amfani da ‘yan kungiyar 33,661 wajen tattaro sauran ‘yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.

A lokacin da yake nasa jawabin bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban Kungiyar Aliyu Liman Bobboi ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.

Ya kara da cewa taron an gudanar da shi ne domin su nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda, sun kuma yi amanna da cancantarsa, suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.

Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shugabanni suna da ta cewa sosai akan wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za su yi ma su biyayya.

Liman ya yi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.

Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.

Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani ya yi tsokaci akan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila dake fuskantar barazana a sassa daban-daban, suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.

Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiwo a duk fadin kasar nan.

A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Tinubu ya yi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ta dindindin.

Ya kara jaddada niyyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiwo na zamani da za su kawo cigaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.

Tinubu ya kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Ya ce wannan abun a yaba ne.

“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya.  Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan.  Ina mai matukar mika godiya da gareku.

“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin,’ a cewar Tinubu.

A nasa jawabin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta, ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.

Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka bashi tareda alkawarin ba zai ba su kunya ba.

Continue Reading

Headlines

Police In Kano arrest two kidnappers, rescue victims

Published

on

Aminu Abdullahi

 

 

 

Kano state police command has arrested 22 year old Nura Auwal, of Rijiyar Lemo Quarters, and his accomplice,  Abubakar Lawal, of Bachirawa Quarters, for the kidnapping of 3 year old Umar Isyaku (3) and 4 year old Aliyu Auwal.

KANO FOCUS reports that the two kidnappers of the children demanded for N20 million ransom, but later settled for N2 million with their parents.

According to Kano state police Command spokesman, Superintendent of Police,  Abdullahi Haruna Kiyawa: “On 26 January, 2023, reports were received from one Isyaku Salisu and Auwal Sale residents of Bachirawa Quarters, Ungogo LGA, Kano State that their children, Umar Isyaku, (3)and Aliyu Auwal (4)  respectively were kidnapped, and handwritten letters with mobile phone numbers and bank account details were sent to them for communication and payment of ransom.

“N20 million was demanded but later settled at Two Million Naira N2 million

“On receipt of the reports, the Commissioner of Police, Kano State Command, CP Mamman Dauda,  raised and instructed teams of Operation Restore Peace led by SP Aliyu Muhammad Auwal, Officer in Charge of Anti-Kidnapping Squad, State Criminal Investigation Department, Kano State Command to rescue the victims and arrest the culprits.

“The teams simultaneously swung into action. Sustained efforts coupled with intelligence-led operations resulted in the arrest of two suspects: one Nura Auwal, (22) of Rijiyar Lemo Quarters Kano, and his accomplice, one Abubakar Lawal, (22) of Bachirawa Quarters Kano.

“Victims were rescued unhurt at an uncompleted building.

“On preliminary investigation, the suspects confessed to having conspired and kidnapped the two children and sent letters to their parents with phone numbers and bank account details requesting a ransom.

“Suspects will be charged to court upon completion of the investigation.”

Continue Reading

Trending