Connect with us

KANUN LABARAI

Bikin Kirsimeti: Bai halarta musulmi ya taya kirista murna ba-Sheik Baban Gwale

Published

on

Zulaiha Danjuma

Fitaccen malamin addinin Islamar nan da ke Kano sheik Abubakar Abdussalam Baban Gwale ya ce bai halarta musulmi na kwarai ya taya kirista murnar bikin kirsimeti ba.

Sheikh Abdussalam na yin wannan bayaninne ya yin zantawarsa da jaridar Kano Focus ranar Alhamis a wani bangare na bikin kirsimeti da ke gudana a yau Juma’a.

Shehin Malamin ya ce ko da yake duk wani abu da bashi da alaka da addini kai tsaye, kamar taya murnar aure, ko haihuwa, samun karin girma wanna ba laifi idan ka taya kirsta murna.

Amma ya ce dukkanin wani al’amiri da ya hada da addini da zai bayu izuwa girmama wancan addinin a kan musulunici to ba halak ba ne ga musulmi.

A cewarsa nuna farincikinka ga addinin kiristanci ya ci karo da koyarwar addinin islama, tunda dai addinin Islam aka ce ka yi riko da shi kai.

“Ba zaman fada ake ba, ana zaman mutunci ne, tayashi farin ciki indan ya samu wani abu na farin ciki kamar aure, promotion, ko haihuwa ba laifi bane.

Amma abun dayashafi krisimeti bai  halalta a taya shi murna ba ko kadan.

“Idan  shi ya taya ka murna a sallar ka, azuminka da laiyyarka, da hajjinka, toh shi wata kila a addinin sa ba a hana haka ba.

“Mu a addininmu cikin suratul Ma’idah, aya ta farko, Allah ya ce kada ku kuskura kuyi musayar amfani, ka amfana a amfanar maka, ka taimaka a taimaka maka akan abun da yake sabone ko kuma zalinci ne.

“Illa iyaka abun da musulmi zai iya yiwa abokinsa wanda ba musulmi ba shi ne, in sun dawo kace musu sannu da zuwa, sannu da dawo wa, kun dawo madallah shikenan.

“Amma abun taya murna na kirsimeti, da zaka fadi abinda suke fada na cewa suna murnan kirsimeti bai halatta ga musulmi ba” A cewarsa.

Ko cin abincin kirsimeti ya halarta

Shehin malamin ya ci gaba da cewa ba laifi ba ne cin abincin kirsimeti sai dai akwai sharruda kafin a kai baka.

Ya ce sharadin shi ne dukkanin naman da aka yanka dan meman kusanci lokacin kirsimeti to wannan bai halarta a ci ba.

Amma idan aka dafa abinci aka cudanya da mana wannan ba matsala ba ne, tunda dai ba naman da aka yanka dan neman kusanci a ka baiwa mutumba.

“Idan an kawo kyautar wani abu na ci ya halatta ka karba, kamar yadda mafi yawan malamai hamshakai, wadanda ke da zurfin ilimi suka bada bayani a cikin littatafan su.

“Abun shi ne naman da aka yanka dan neman kusanci wannan bai halatta mutun ya ci ba.

“Amma  abinda  ya halatta mutun ya ci shi ne abinci, misali abinci da nama, dama duk abunda aka hadashi da abinci wannan ba zai zama da matsala ba, tunda ba za a ce ka ci nama ba, abinci kaci kuma a ala’dance akan ci abinci hade da nama”

“Bisa al’adarmu a musulunce ai idan akayi yanka kuma akan farfasa naman ko a dafashi ko a soyashi sannan ayi kyautar sa.

“To suma  zai iya zama haka a al’adar su, tunda akan samu hakan wani lokaci, wasu al’umma addininsu yana haduwa da al’ada sai kaga yadda abokanan zamansu musulmi ke yi suma haka suke yi.

“Ayi yanka a babbaka washegari a sassara sannan a soya a rabar irin wannan shi ne baza ka ci ba”

Ko musulmi zai iya yankawa kirsta dabba?

Malamin yaci gaba da cewa yin hakan ya danganta da dalili yankan da kuma niyar yin yankan.

Ya ce matukar yanka dabbar ka iya bayuwa izuwa ibada da neman kusanci ga Yesu al-masihu to ko kusa wannan yanka bai halartaba.

Ya ce amma yanka ba na ibadaba, kamar a ce kirista ya zo da kaza ko wani rago a yanka don a ci ba neman kusanci ba to wannan babu laifi.

“Idan dai ba yanka ne na ibadah ba, musulmi za iya tallafawa, kamar a ce  anyi dan a ci abinci dashi, misali sunzo  da kaji ko rago dan su dafa suyi abinci wannan ba laifi za ka iya taimakawa tunda suna yin haka”

“Amma idan yankane na ibadah kamar yadda mu layya yanka ne na ibadah, suma kuma suna da yankan ibadah, to idan yanka ne na ibadah ko na neman kusanci zuwa ga Yesu al-masihu to bai halatta ka shiga cikin wannan abun ba” A cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending