Connect with us

KANUN LABARAI

Direbobin manyan motoci a Kano sun zargi jami’an tsaro da karbar cin hanci da rashawa

Published

on

Direbobin mota a tashar Kano Line sun zargi jami’an KAROTA da ‘yan sanda da kuma hukumar Road Safety da tilastamusu bada cin hanci da rashawa.

Kano Focus ta ruwaito direbobin na cewa jami’an tsaron na karbar musu kudi naira dubu dai-dai a duk lokacin da za su shigo jihar Kano da safe.

Wani mai suna Abubakar Yusuf ya ce a duk lokacin da suka ki bayar da na goron, jami’an na kaisu ofis tare da rubuta musu wani laifin na daban da sunan cewa ya karya doka.

“Idan muka zo U-turn wanda daga shi sai Kano Line za ka shiga ka sauke fasinjanka wani lokacin akwai MTD suna yawan uzura mana.

“A kwai KAROTA akwai Road Safety, wani zubin kamen na ba gaira ba daliline za a zo a ce an kama ka, suna iya karbar dubu daya dubu daya da dari biyar,” a cewar sa.

Shima Husaini Adamu ya ce ya kamata akai musu dauki la’akari da cewar basu da wurin da yawuce nan domin gudanar da sana’o’insu.

“Baki suna shigowa amma sakamakon irinhaka yanzu duk sun hakura sun daina shigowa,” a cewar sa.

To sai dai kan wannan zarigine muka tuntubi hukumomin da ake zargi da karbar na goron a hannun direbobin inda kuma sukayi bayani.

Mai Magana da yawun hukumar Road Safety a  jihar Kano Kabiru Ibrahim Daura ya ce matukar direba ya karya doka dole za a kamashi.

Sai dai ya ce kamata ya yi masu korafin su je kai tsaye ofishin hukumar, su kai korafinsu matukar ana kamasu ba da hakkinsu ba.

“Amma idan laifi sukeyi aka kamasu kaga wannan ba abin yin korafi bane, sai dai mu basu shawara su daina aikata laifin.

Haka zalika itama hukumar KAROTA cewa ta yi masu korafin suna ajiye motocinsu ne a kan hanya bayan kuma haramunne yin hakan.

Mai magana da yawun hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa  ya ce babu wani jami’insu da zai ce a bashi kudi a hannu ya saki wani mai laifi ba tare da anje office ba.

A nata bangaren rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce batada masaniya kan zargin.

Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar ya ce kamata ya yi direbobin su kai korafinsu ga shugabanin kungiyoyinsu ko rundunar ‘yan sanda kai tsaye.

Sai dai ya ce tun da sun samu korafin to za su bincika gaskiyar lamarin tare da daukar matakin da ya dace

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending