Connect with us

KANUN LABARAI

Matashi a Kano ya yi yunkurin kashe abokinsa kan N800

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar’ yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai suna Dini Abdullahi da ya yi yunkurin kashe wani Ahmad D Ahmad bayan da ya caka masa kaho a idonsa da kuma kirjinsa a unugar Diso.

Kano Focus ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abdullahi Haruna Kiyawane ya sanar da hakan a ranar Talata.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘ya sanda ya ce wanda ake zargin ya soke shi ne bayan da rigima ta kaure a tsakaninsu kan bashin naira dari takwas.

Dini ya ce yana bin Ahmad bashin kudi N800 ne, inda shi kuma ya musanta, da hakan ta sanya suka fara rigima,  har ya yi amfani da damar wajen raunata abokin fadan nasa.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya gargadi sabbin ‘yan sandan cikin al’umma kan cin hanci

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da attajirin Minjibir da aka yi garkuwa da shi

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da attajirin Minjibir da aka yi garkuwa da shi

Ya kara da cewa tuni suka kama wanda ake zargin kuma ya tabbatar musu da cewa yana shan wiwi da kwayoyi.

Ya kumace wanda ake zargin Dini Abdullahi ya amsa laifinsa, inda tuni kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a mayar dashi sashen binciken manyan laifuka na kisan kai domin a fadada bincike.

A nasa bangaren wanda ake zargi Dini Abdullahi ya ce ya caka masa kahonne saboda yaki biyansa bashin da yake binsa.

“Dokin zuciya muka hau gaba dayanmu kuma da nasan haka za ta faru wallahi bazanyi mas ba,” a cewar sa.

Shi ma wanda aka raunata Ahmad D Ahmad ya ce a saninsa babu wani abu a tsakaninsu kawai dai ya tsinci kansa ne a gadon asibiti.

“Ya cakamin a ido da kirji na da kuma sauran sassan jiki na, da farko bansan mai yake bugamin ba, ina ta rikeshi ya ki dainawa kuma ni bayabina ko sisi,” Inji shi.

Ya kuma bukaci mahukunta dasu bi masa hakinsa duba da yadda aka zalince shi ba tare da laifin komai ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending