Connect with us

KANUN LABARAI

Bakin talauci yasa an bude tashar ‘Buhari’ a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Anbude wata tashar mota a nan Kano da ake kira tashar Buhari, a kan titin France Road  da ke yin amfani da akori-kura domin daukar fasinjoji zuwa unguwar Rijiyar Lemo.

A wata tattaunawa ta musamman da Kano Focus, shugaban tashar Malam Mani ya ce tashar ta samo sunanne  daga halin matsin tattalin arziki da kasar nan ke ciki a zamanin mulkin Muhammadu Buhari.

Malam Mani ya ce  tashar ta fara aikine shekara hudu da suka shude, domin magance matsalar da al’umma ke fuskanta na na tsadar rayuwa.

Ya ce galibin wadanda ke hawa motar a tasharsu ko kudin adai-daita sahu da taksi ba za su iya biyaba.

Ya kuma ce kafin bude tashar yawancin mutanen dake unguwannin nayin tafiyar kafa daga guraren kasuwancinsu zuwa gidajen su.

Amma bayan bude tashar, mutane musamman tsofaffi da yara na samu su isa gidajensu akan kudi da bai wuce naira arba’in ba wani lokacin ma kyauta.

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umarnin bude iyakokin kasar nan

Za a bude iyakokin kasar nan ba da jimawa- Muhammadu Buhari

Matsalar tsaro: ‘Yan wasan Hausa a Kano na caccakar shugaba Buhari

“Baya ga wahalar da ake ciki yawancin al’ummar da ke unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo da kuma Bachirawa na da matukar yawa ta yadda wasu ke kiran yankin ‘China’ hakan tasa dole suke hawa motocin namu.

“A da ni direban babbar mota ne amma na zama shugaban wannan tasha bayan da na rasa motata kuma na shawo kan abokan sana’ata don su zo su taimakamin a wannan tasha wanda dasune muke gudanar da sana’ar tare,” a cewar sa.

Shima wani direba mai suna Muhammad Jamilu ya ce sakamakon bude tashar a yanzu yana samun kudin siyawa iyalan sa biredi da gawayi don yin girki da kuma alawa ga yaran sa.

“A kasuwar kofar ruwa nake sana’ata, amma a Bachirawa nake zaune. Ina zuwa nan da yamma domin na dauki fasinjoji kuma ina samun a kalla naira #700 zuwa naira #800 a kowace rana.

“Haka kuma da safe ma muna daukar mutane daga Rijiyar Lemo zuwa wannan Tashar,” a cewar sa.

Wani fasinja mai suna Ibrahim Lawan ya ce kafin bude tashar yana tafiya a kafa zuwa kasuwa ko dawowa a duk lokacin da bashi da kudin mota, amma a yanzu da naira talatatin kacal yana iya komawa gida daga kasuwa.

Ya kara da cewa wahalar da wannan gwamnati ta haddasa shi ne abinda ya janyo wadannan matsaloli don kuwa komai ya canza.

Ya ce sai suna zuwa  kasuwa tun safe har yamma amma ko kwandala basa samu hakan yasa suke tafiya a kafa.

Salisu Sani cewa ya yi talauci da yawan jama’a dake Kurna yasa mutane ke rububin hawa manyan motocin kuma mutane da kansu ne suka sanyawa gurin suna Tashar Buhari.

“Na rasa Adaidaita Sahun da zai kaini a kudin da nake da shi kaga bani da zabi dayawuce na hau kurkura na koma gida don bazan iya komawa a kafa ba,” a cewar sa.

Sai dai ya ce hawa motocin na Kurkura da Akori kura na da hadari domin kuwa wasu na amfani da damar wajen yin sata.

“Nasan mutumin da aka sacewa naira dubu goma a cikin motar, kaga yaki biyan naira dari biyar yahau Adaidaita Sahu saboda mammako.

“Kuma wasu lokutan zakaga gefen wata motar ba a rufe yake ba wanda hakan ka iya haddasa asarar rai idan mutum ya fado yayin da ake tafiya,” a cewar Salisu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending