KANUN LABARAI
An samu karancin fitowar Jama’a a za6en Kano
Aminu Abdullahi
An samu karancin fitowar mutane zuwa filayen kada kuri’a a mazabar Tukuntawa dake karamar hukumar birnin Kano.
A zagayen da Kano Focus ta yi a ranar Asabar ta lura da rashin fitowar al’umma, ya yin da a gefe daya kuma su ma jami’an zabe ba su isa filayen zaben akan lokaci ba.
A mazabar Tukuntawa jami’an zaben sun isa rumfunan za6en ne da misalin karfe 11:30 na safe, inda aka fara kada kuri’a da karfe 12:25 na rana.
Haka zalika Kano Focus ta gano yadda aka kebe wasu mutane da suka rika yin dangwale ga wata jam’iyya mai fada a ji a kwatu mai lamba 26 da 27 dake mazabar.
Wani matashi da ya zo kada kuri’a Hamisu Umar cewa ya yi ya kada kuri’ar sa ba tare da bata wani lokaci ba, sai dai ya ce akwai dakunan da ya tarar masu aikin zaben ne da kan su suke dangwalawa wata jam’iyya.
“Ya wancin wadanda suka je da niyyar yin zabe basu fi mutum 20 ba ragowar duk ma’aikatan zabene da jami’an tsaro da kuma wakilan jam’iyar APC,” a cewar sa.
Shi ma Yusuf Abubakar ya shaidawa Kano Focus dama shi bai dauki zaben a matsayin wani zabe na a zo a gani ba duba da yadda aka samu karancin masu fitowa.
Ya ce koda ya zo, wasu ya tarar a akwatinsa suna ta yin dangwale sai dai yana kada kuri’a sai ya bar wurin.
“Kuma ka ga dai-dai-kun mutane ne ke sanye da takunkumin rufe baki da hanci.
“Gaskiya ba zan kara yin zaben kananan hukumomi ba,” inji Yusuf.
Wata mata da Kano Focus ta gani a rumfar za6en, Hadiza Ibrahim cewa ta yi “Ni nazo ne na kora yara na zuwa gida.”
Ta kara da cewa tana da katin zabe, amma mijinta ya ce sam kada taje ta zabi kowa.
“Ko kai yanzu kaga babu wata macen arziki data fito yin zabe, akan me to ni zan fito,” a cewar ta.
Sadiq Abubakar ya ce zabe yana tafiya daidai kamar yadda suka yi tsamani, sai dai ya ce duk da rashin fitowar al’umma, an samu zaman lafiya.
“Tun da nazo gurin nan ba wanda ya zagi wani kowa yana yin zabe cikin kwanciyar hankali, wannan shi ne abun da ake so dama,” a cewar Abubakar Sadiq.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.