KANUN LABARAI
Mai ya kamata ku sani game da tallafin gwamnati na kiwon jaki-Sheik Daurawa
Aminu Abdullahi
Fitaccen malamin addinin musulunci a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce haramun ne musulmi ya karbi tallafin kudaden da gwamnati ko bankuna ke bayarwa don kiwon jaki.
Malam Daurawa ya bayyana hakanne yayin zantawarsa da Kano Focus a ranar Litinin.
Wanna dai na zuwa ne bayan da aka yiwa malamin fatawa kan shirin gwamnatin tarayya na baiwa jama’a tallafi domin gudanar da kiwo jakuna.

Ya ce noman jaki ya kasu kasha biyu, akwai noman jaki da akeyi ta hanyar da shari’ar ta amince, shi ne daukar kaya da sauran abubuwa da jaki yakeyi na al’ada.
Sannan kuma akwai noman jaki domin safararsu ga masu ci ko yankawa domin wata bukata.
Ya kara da cewa jaki dadadden abune wanda Allah S.W.A ya ambace shi a cikin alqur’ani, a gurare da dama kuma manzon Allah S.A.W yana da jaki hakama sahabban sa.
Tsohon gwamnan Kano Kwantagora ya rasu
Jahilai ke sukar Fatawar Dr Bashir kan sakin aure a film-Sheikh Umar Sani Fagge
Duk wanda ya saki mace a film ta gida ta saku-Dr Bashir Aliyu Umar
“A kwai lokacin da aka zo yakin Khaibara saboda yunwa da ta damu sahabbai, har akayi tunanin a yanka jakuna a ci, kuma aka yanka jakunan aka dora sanwa, saida ya tafarfasa ya dauko dahuwa sai annabi S.A.W ya bada umarnin cewa a zubar da naman a fasa tukunyar.
“Sai wani sahabi yace ko a wanke? wannan ya nuna cewa anyi yunkurin cin naman jaki annabi ya hana kamar yadda ya tabbata a hadisai ingatattu, a cewar sa.
Malamin ya ce tabangaren abinda ya shafi hukunci an haramta cin jaki a musulunci duk da cewa an samu kauli hudu a cikin mazahabobi akwai mazahabar da ta tafi akan cewa cin jaki haram ne.
Haka zalika yace akwai malaman da sukace cin jaki halal ne, wancan da aka hana an hana ne akan cewa kada a cinye jakuna a wancan lokaci ya zama babu abin hawa.
“Akwai kuma malaman da sukace makaruhine, kamar a mazahabar malikiya, an kawo ruwaya biyu wasu sunce cin jaki makaruhi ne wasu kuma sun ce halal ne,” inji Daurawa.
Sai dai ya ce abinda aka tafi akai shi ne hadisi karara da ya ce annabi S.A.W ya haramta cin naman jakin gida da auren mutu’a .
A don haka idan har gwamnatin tarayya ta baiwa mutum kudi ya kiwata jaki domin suyawaita a cikin al’umma kuma ayi ayyuka dasu irin na al’ada to wannan babu laifi.
Haka zalika ya ce idan mutum ya yi kiwon jakuna domin a rinka siyarwa wadanda za su ci to tamkar yatemakane a ci jakin dashi, kuma addini ya hanashi ya ci ko ya siyar aci.
Ya kara da cewa musamman wadanda suke kaisu kasar China ana kashe su anaci, sannan ayi amfani da fatun su wajen yin wasu sinadarai na magunguna to sun sabawa koyarwar addinin musulunci kuma Allah zai tambayesu akan hakan.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
