Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan sanda sun kama mace mai garkuwa da mutane a Kano

Published

on

KEDCO-Nigeria

Mukhtar Yahya Usman

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wata mata Maryam Muhammad da ke yin garkuwa da mutane a nan Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewar a ranar Juma’ar da ta gabatane rundunar yan sandan ta yiwa wani gida tsinke da ake zargin maboyar masu garkuwa da jama’a ne a unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo.

Ya yin sumamen rudunar ‘yan sandan ta samu nasarar kama mutane hudu da ake zargin masu garkuwane ciki har da mace guda daya.

Jami’in hulda da jama’a na rudunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya  ce rundunar ta yi nasarar kama  maza uku da mace daya a cikin gidan.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da matashin da ya yi yunkurin hallaka kansa.

‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda suka hallaka dattijo a Kano

Gobara ta kashe mutane uku ‘yan gida daya a Kano

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce biyu daga cikin wadanda aka kama din yan asalin jihar Zamfara ne.

Ya ce bincikensu ya gano cewar wadda aka kama din mai suna Maryam ta ce ta karbi hayar gidan akan kudi dubu dari shida ko wacce shekara.

Ya ce Maryam ta shaida musu cewa ta shiga harkar garkuwa da jama’a bayan da aka kashe mijinta da shima barawon shanune a jihar Zamfara.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending