Connect with us

KANUN LABARAI

Jahilai ke sukar Fatawar Dr Bashir kan sakin aure a film-Sheikh Umar Sani Fagge

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke nan Kano Sheikh Umar Sani Fagge ya ce marasa Ilimi ne ke sukar fatawar Dr Bashir Aliyu Umar da ya ce duk wanda ya saki matarsa a film to ta gida ta saku.

Kano Focus ta ruwaito malamin ya yi wannan bayanine ta cikin wani fai-fafan bidiyo mai munti 1:30 da aka wallafa a shafin facebook ranar Litinin.

Malam Umar Sani Fagge ya ce duk wanda ya soki fatawar Dr Bashir Aliyu Umar to ya nuna baya karatu kuma bai san darajar malamata ba.

Idan za a iya tunawa dai Dr Bashir Aliyu Umar da ke zaman babban limanin masallacin juma’a na Alfurqan ya ce duk wanda ya saki mace a cikin shirin film to dai-dai yake da sakin matarsa ta gida.

Shehin malamin ya ce duk wani danwasa da ya furtawa matarsa ta film saki, to ba bu shakka ya saki matarsa ta gida, kuma babu aure a tsakaninsu.

“Kodawasa idan kazo aka daura maka aure a film, mutum ya ce ya saki matansa kuma yana da mata, kuma ya fada ya ce ai matan nawa duk na sake su, wai yana nufin matansa na wasan Hausa, to na gasken sun tafi.

“Ba a wasa da sha’anin saki, ko kuma aure, kazo a cikin wasan Hausa a ce an daura maka aure, sannan kace kuma wannan ba aure ba ne? kuma an daura aure an cika sharadan aure, to aure ya dauro.

To sai dai wannan fatawa bata yiwa jama’a da dama dadiba, musamman masu sana’ar film.

Hakance ta sanya jama’a suka fara surutai da sukar malamin a shafukan sada zumunta na facebook da sauransu.

Sai dai Malam Umar Sani Fagge ya fito ya baiwa malamin kariya, inda ya ce fatawarsa na kan dai-dai.

Har ma ya kawo hadisai da suka dace da fatawar, inda ya ce bisa doron hadisin, saki baya la’akari da niyya, indai anyishi ko da wasa to ya tabbata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending