Connect with us

KANUN LABARAI

Tsadar man kuli ta sabba hauhawar farashin kosai da awara a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Hauhawar farashin man gyada a Kano ya sabba karuwar farashin kosai da awara da sauran kayan da ake sarrafawa da man gyada.

Kano Focus ta ruwaito a ‘yan kwanakin nan kosai da awara da fanke suka yi tashi gwauron zabo sakamakon karuwar farashin man gyada a fadin jihar.

Binciken da Kano Focus ta gudanar ta gano cewar a baya dai ana sayar da kwalbar man kuli akan N450, da a yanzu kuma ake sayarda kowacce kwalba akan N650 zuwa N700.

Haka zalika a yanzu ana sayar da karamin galan  akan N5500, sabanin yadda ake sayar dashi a baya da bai gaza N300 ba.

Kosai N10 duk guda daya

Hajiya Aisha Sulaiman wata mai sana’ar tuyar kosaice a nan Kano, ta ce ya zama dole ta mayar da sakin kosai daga N5 zuwa N10 sakamakon tsadar da man gyada yayi.

A cewarta matukar bata kara farashin ba to ba za ta iya mayar da kudin da ta kashe ba ballantana ta ci riba.

“Ya zama dole nayi hakan, idan ba haka ba bazan maida kudina ba.

“Wake ya yi tsada, muna siyan kwano akan N800 ga kuma mai shima yadda kullum yake kara kudi.

“Mankuli ma ana saida shi ne akan N800, to kaga bamu da zabi tunda ba zamuyi tuya da manja ba.” a cewar ta.

Biyu 50 muke sayar da fanke 

Ita ma Rukayya Muhammad da ke zaune a unguwar Tukuntawa dake sana’ar tuyar fanke ta ce kafin karuwar farashin mangyada tana saida fankenta akan naira goma duk guda daya.

Sai dai ta ce a yanzu dole ya sanya take sayarwa aka N50 duk guda biyu.

Ta ce duk da ta kara kudin amma mutane na cigaba da zuwa siya sai dai ba kamar a bayaba, lokacin da take sayarwa akan N10

“Ni kaga jarka nake siya amma wallahi a hakanma dakyar nake maida kudi na, kaima dai kasan yadda abubuwa suke tsada kulllum abubuwan kara kudi suke yi.

“Wasu idan suka zo siya dana fada musu yadda na koma siyarwa sai suyi tafiyar su, basa dawowa, don ranar da na fara canza farashi ma saida nayi kwantai,” a cewar ta.

Munfi sayar da awara akan uku N50

Talatu Gambo dake sana’ar a wara akan titin Gidan Zoo ta ce duk da kudin wake ya karu amma tana siyar da a wararta duk guda daya akan naira goma.

Sai dai ta ce a yanzu da farashin mangyada ya karu ta koma siyarwa akan guda uku naira hamsin.

“Saboda a gefen titi nake ciniki, shiyasa koda na sauya farashi ana cigaba da siya,

“Haka kuma ko yanzu farashin ya ragu to nima zan rage nawa farashin ya koma kamar da.

“Ni dai dana tambaya meyasa kudin mangyadan ya karu sai aka cemin wai yanzu ba a noma gyada, a kasar nan yawanci ana kawo ta ne daga Senegal,” a cewar ta.

In makomar jama’a?

Jama’a da dama da Kano Focus ta zanta dasu kan wannan kari da aka samu, sun nuna rashin jin dadinsu da halin da aka tsinci kai a ciki.

Wani matashi Ibrahim Isma’il da muka iske a layin siyan kosai yace kwanaki uku da suka gabata N5 ya sayi kosan duk guda daya sai dai yanzu ya koma N10.

“Kwana uku da nazo na siyi kosai duk daya N5, amma a yau da na dawo ana saida guda daya N10.

Haka na hakura nasiya saboda iyalina ta damamin koko kuma ba zai shawu ba babu kosai.

“A da ina siyan na N200 amma yau sai da na siyi na N500 saboda farashi ya tashi.” inji Ibrahim Isma’il.

Abubakar Abdulaziz da muka tarar shima yaje siyan kosai cewa ya yi ba zai iya siyan kosai ba a halin yanzu , duba da yadda aka kara masa kudi.

Ya ce ada yana siyan na dari da hamsinne wanda ake bashi duk guda daya a N5 sabanin yanzu da aka ce masa N10.

Ko hakan ya shafi mata a gida?

Sadiya Hassan uwargidace da ke zaune a unguwar Tukuntawa ta ce a yanzu ba a samun man gyada na N50 sabanin yadda a baya ake basu

“A watannin baya N50 ko N100 ta isheni nayi miyar kuka ko miyar shinkafa, amma yanzu sai na saka N150 nake iya siyan man da zanyi girki dashi.

“Kuma kudin cefanen da ake bamu ba karuwa yayi ba, a haka muke riritawa mu girka koda babu dadi don girki ba zai yiwuba idan babu mai, shi kansa yanzu manjan tsada yake yi,” inji Sadiyya.

Jamila Muhammad cewa ta yi a yanzu suna yin girkine  kawai da hikimomi tunda dai abubuwa sun ta’azzara.

“Gaskiya ni kaga mai gidana baya son girki da manja, kuma yanzu mangyadan ya yi tsada, hakuri kawai ake y, ni a yanzu ma nafi jika garin kwaki musha da yarana, saboda tsadar da man yayi,” a cewar ta

Ko me dillalan man ke cewa?

Abdullahi Adamu dake sana’ar sayar da mangyada a kasauwar Rimi ya ce watanni biyu da suka gabata suna siyar da mangyada duro guda akan N170,000, amma a yanzu suna sayarwa ne aka N190,000.

Ya kuma ce suna sayarda yaluwar jarka akan N19,500, sai kuma karamin galan suna sayarwa akan N4000 sai kuma kwalba daya akan N650.

Ya kuma ce tashina man na da nasaba da gyadar da ake sarrafawa domin yin mangyadar, ana shigo da ita ne daga kasashen ketare.

A cewarsa hakan ya farune  sakamakon karancin noman gyada a jihar nan da ma kasa baki daya.

Saidai ya ce farashin yana hawa da sauka ne a galibin lokuta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending