KANUN LABARAI
Mata a Kano na murna da kulle gidajen Kallo
Aminu Abdullahi
Mata da dama ne a nan Kano ke nuna farincikinsu tare da yabawa gwamnati kan matakin da ta dauka na kulle gidajen kallo a daukacin jihar nan.
Kano Focus ta ruwaito galibin matan na korafin yadda mazan ke shigar musu hakki matukar aka ce ana wasan kwallon kafa.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da jama’a ke ci gaba da kiraye-kirayen a bude gidajen Kallon.
A cewarsu kulle gidajen kallon ba abin da zai haifar sai jefa al’umma cikin kunci da damuwa.
Gidan kallon ball na raba soyayya
Hussaina Adam wata budurwace a nan Kano ta ce gidan kallon ball ya sha sanyata fada da samarinta, a cewarta indai aka ce akwai ball to ko ba yadda za a yi samarinsu su je zance wurinsu.
“Duk lokacin da zaizo gurina matukar ya yi dai-dai da lokacin da za a haska wani wasa a gidan kallo baya zuwa.
“Sai ya ce min zaije kallon wasan Manchester, ko Real Madrid, a karshe ma sai dai mu sake tsai da wata ranar.
A gaskiya gidajen kallo na bata min rai,” a cewar ta.
Sakina Abdulmalik wadda matar Aurece ta ce, mijinta baya zama a gida da daddare matukar za a yi wani wasa to zai tafi gidan kallo.
Ta kara da cewa da zarar yadawo daga kasuwa da yamma, a nayin salar magriba yake fita zuwa gidan kallo, kuma ba zai dawo ba sai kusan karfe goma sha biyun dare.
“Kaga duk sanyin nan da akeyi sai yaje, amma jiya da daddare ba inda ya fita saboda an rufe gidajen kallon, wannan hukunci ne mai kyau,” a cewar ta.
Nafisa Tijjani itama wata budurwace a nan Kano, ta ce ta rabu da samari da dama sakamakon zuwa gidan kallon kwallon kafa.
A cewarta lazimtar kallon da suke yi ya sanya bata samun kulawar daga gare su.
Ta kuma ce idan da ace gwamnati za ta rufe gidajen kallon har a bada ma da tayi farin ciki da haka.
“Mu mata masu aure da marasa aure bama jin dadin gidajen kallon nan wallahi,” a cewar Nafisa.
Maza za su damemu da zaman gida
Su kuwa wasu matan cewa sukayi bai kamata gwamnati ta rufe gidajen Kallo ba domin wata hanya ce da ke samarwa maza nishadi.
Khadija Abba Garba ta ce kokadan bata ji dadin rufe gidajen kallon ba domin yana samar da nishadi.
Ta ce yanzu da aka rufe gidajen kallon mazajen su za su dinga damunsu da zaman a gida su kuma fara sa musu ido.
“Nikam bana goyan baya gaskiya, kaga wani lokacin ma mai gidana yana tafiya dani classic gurare da ake kallon kwallo.
Ko ina ra’ayin samari?
Sai dai a nan kuma magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano ne ke cigaba da kokawa kan yadda gwamnatin ta kulle gidajen kallon.
Hassan Ibrahim cewa ya yi baya goyan bayan rufe gidajen kallon duba da yadda harkokin wasanni ke daukewa matasa kewa tare da kara hadin kai a tsakanin su musamman idan suka je gidajen kallon kwallon kafa.
Ya kara da cewa idan har yazama dole a rufe gidajen kallon to yakamata gwamnatin ta raba musu da ta wacce za su rinka yin amfani da ita don kallon wasannin da akeyi ta shafukan internet.
“Ni kaga bamu da dammar da zamu iya kallon wasan kwallon kafa a gida don ba zamu iya siyan kati ba kuma ni masoyin kungiyar Manchester ne dole idan inaso na kalli wasan mu to sai nazo gidan kallo.
Aliyu Rabi’u Neymar ya ce bashi da gurin da a yanzu zai samu ya rinka kallon wasannin da ake haskawa na gida da na waje kasancewar an rufe guraren dake haska wasannin.
“Kaga dai bani da ilimin boka balle na kalla ta yanar gizo kamar yadda wasu ke cewa za su koma kalla ta internet to mu ya za ayi damu kenan.
“Idan nadawo daga gurin aiki idan dare yayi ba indai nake samun nishadi sama da gidan kallon, a cewar sa.
Muzammil Umar ya ce a yanzu zai koma kallon wasannin ne a gida tare da iyalansa saidai ya ce kallo a cikin mutane da yawa yafi dadi.
“Duk lokacin da na kalli wasa a gida bana samun nishadi kamar yadda zan fita waje. a kalla a cikin abokanai na muyiwa juna ruba,” a cewar sa.
Isma’il Kabuga ya ce rufe gidan kallo zai kawo koma baya ga harkokin wasannin ga matasa kasancewar gidajen kallon na debe musu kewa idan suka dawo daga kasuwa ko gurin aiki.
“Rufewar ba alheri bane don yanzu wasu za su koma zaman majalissa ai ta musu wanda daga karshe ma ai ta samun rigima a tsakanin.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.