KANUN LABARAI
Yadda kawuna ya turoni Kano domin garkuwa da mutane
Mukhtar Yahya Usman
Maryam Muhammad shahararriyar mai garkuwa da mutane, yar asalin jihar Zamfara ta ce kanin mahaifiyarta mai suna Dogo Hamza ne ya sanyata cikin aikin garkuwa da mutane.
Kano Focus ta ruwaito Maryam na wannan jawabin ne ga manema labarai bayan da rundunar ‘yan sandan Kano ta yi holinta da abokan sana’arta ranar Laraba a nan Kano.
Idan za a tuna a makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama Maryam Muhammad da ta kware wajen garkuwa da mutane.
A cewar rundunar yan sanda tun a ranar Juma’ar da ta gabatane ta yiwa wani gida tsinke da ake zargin maboyar masu garkuwa da jama’a ne a unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo.

Ya yin sumamen rudunar ‘yan sandan ta samu nasarar kama mutane hudu da ake zargin masu garkuwane ciki har da Maryam da ke zaman shugabarsu.
Jami’in hulda da jama’a na rudunar ‘yan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ta yi nasarar kama maza uku da mace daya a cikin gidan.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da matashin da ya yi yunkurin hallaka kansa.
‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda suka hallaka dattijo a Kano
Gobara ta kashe mutane uku ‘yan gida daya a Kano
Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce biyu daga cikin wadanda aka kama din yan asalin jihar Zamfara ne.
Ya ce bincikensu ya gano cewar wadda aka kama din mai suna Maryam ta ce ta karbi hayar gidan akan kudi dubu dari shida ko wacce shekara.
Sai dai da take amsa tambayoyin manema labarai a yau Laraba Maryam ta ce ta taso a hannun kawunta ne da shima kasurgumin barawon shanune tun tana yarinya har ya yi mata aure.
Haka zalika ta ce kawun nata shi ne ya aurar da ita ga wani mutum wanda shima barawon shanune.
Maryam ta ce bayan da aka kashe mijin natane a wajen satar shanu, kawun nata ya umarce ta da ta taho Kano ta kuma tayashi a cikin ayyukansa na garkuwa da mutane.
Ta ce bayan ta dawo Kanone kuma ya aiko mata da masu tayata aikin, maza guda biyu da suka hadarda Sani Ibrahim da Shamsudden Sulaiman.
Ta ce bayan ta zo Kano ta fara garkuwa da mutanene ta ke aikewa da kawunata bayanin wanda aka kama, shima ya kira dangin sa ya nemi kudin fansa.
Ta kara da cewa ta fara garkuwa da wani matashi mai suna Muhammad Sunusi dan asalin karamar hukumar Gwale inda suka nemi kudin fansa N10million.
Haka zalika ta ce bayan da ta kama na biyunne kuma wanda abokin huldartane da ke sana’ar sayar da waya, ta kuma nemi kudin fansa N5million, kafin a kai ga biya jami’an yan sanda suka cimmata.
“Kawunane Dogo Hamza ya sani cikin harkar, a hunnusa na taso a hannusa na girma, shi yayi mini aure.
“Shi ne ya ce min bayan an kashe mijina na shigo cikin gari in zauna.
“Na kira saurayina mai sayar da waya nace ya kawo min waya, bayan ya kawo min ne sai shanmsu ya kamashi.
“Gaskiyar Magana mun tsara za mu kamashi, shi yasa muka hada baki da su shamsu muka gayyato shi.
“Ban san ko nawa aka nema ba kawuna ne yake kira yana Magana akan kudin fansa ban san ko mawa ya nemaba.
“Amma bamuyi maganar za a kasheshi ba kamashi kawai muka yi don ya bamu kudi.
Haka zalika maryan ta ce kawunta ya turota Kano ne badan tayi garkuwa da mutane ba, daga baya ne ya turo mata wadanda za su taya ta.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
