KANUN LABARAI
Idan muka fara ramuwa a kan ‘yan kudu abin ba zai yi dadi ba-Bashir Tofa
Aminu Abdullahi
Shugaban kungiyar dattawan Arewa Alhaji Bashir Othman Tofa yayi Alawadai da kinsan da ake yiwa ‘yan arewacin kasar nan musamman Fulani a kuduncin kasar nan inda ya ce matukar aka fara ramuwa to za a sha wahala kafin a shawo kan al’amarin.
Kano Focus ta ruwaito cewa Tofa ya bayyana hakane cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata a nan Kano.
Ya ce ba abune da za a yarda dashi ba yadda ake kashewa tare da raunata al’ummar Arewacin kasar nan a yankin kudancin kasar.
Ya ce a bayyana yake cewa akwai mumunan shiri da wasu keyi da zai haifar da rikici da ka iya sanadiyyar ruguza kasar baki daya.
“Abubuwa sun fara daukar dimi matukar ‘yan Arewa suka fara daukar fansa akan al’ummar kudu dake zaune a nan tofa zai yi wuya a shawo kan al’amarin.
“Makiya na gida da na waje, wasu ma jami’an tsaro sun san su, suna kulla kullar yadda zamu ci zarafin junanmu, ta yadda ba zamu sake dawowa kamar yadda muke ba da zarar an fara zubda jini.
“Babu wani bangare a kasar nan da yake zaune lafiya.
“ ‘Yan ta’adda na cikin gida da makota dama na kasashen ketare nata kokarin yin duk mai yiwuwa don ganin sun ruguza mana kasa,” a cewar sa.
Haka zalika yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matsalar tsaro da ta addabi kasar nan da kuma yadda ake kashe mutane ba gaira ba dalili da muhimmanci tare da daukar mataki na gaggawa don magance su.
“Nasan fadar shugaban kasa ta damu kuma ana tattaunawa akan batun amma akwai bukatar daukar matakai na gaggawa.
Ya kara da cewa idan har wani dan kasar nan ba shi da ikon yin rayuwa da gudanar da kasuwancinsa har sai an muzguna masa ko yi masa barazanar kisa a wani bangare na kasar nan, to babu wani mahaluki da yakamata a bari shima ya zauna a ko ina.
“Idan kuwa har hakane to bamu da kasa kuma wannan shi ne abinda makiyanmu ke fata kuma bai kamata mu bar suba.
“Wadancan shugabanni wawayene suda ‘yan amshin shatansu wadanda ke karfafa musu gwiwa korar wasu ‘yan kasa daga jihohin su,
“Ya kamata su tuna cewa suna da ‘yan uwa dake zaune a wasu sassan arewacin kasar nan.
“Dole ne su daina, ko kuma doka ta dakatar da su ta hanyar da ya dace,” a cewar sa.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.