Connect with us

KANUN LABARAI

Malam Kano kada kuyi mukabala da dan shi’a-Dr Gumi

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi kira ga malaman Kano da su kauracewa yin mukabala da Sheik Abduljabbar Kabar tunda dai ta bayyana dan shi’a ne.

Sheikh Gumi ya bayyana hakanne ta cikin karantun da ya saba gudanarwa a majalisinsa ranar juma’a a garin Kaduna.

Ya ce dukkanin dalilai sun tabbata Abduljabbar dan shi’a ne to kuwa malaman za su bata lokacin su ne kawai domin ba za a samu fahinta a tsakaninsu ba.

“Shi ya bayyana dan shi’a ne, saboda haka dan shi’a ba zai zo cikin littattafan sunna ya yi munazara da ‘yan sunna ba.

“Sai dai ya dauko nashi littattafai na shi’a.

“Su kuma za su  dauko nasu na sunna ne, amma ba zaka shigo cikin suna da litattafan shi’a kace zakayi munazara da ‘yan sunnaba.

“Domin kuna bashi shar’iyya, kuna bashi marja’iyya, wadda bai da ita.

Ba inda ya koyi wannan ilimin shima ya koyi wannan Ilimi ne, magen waje ce, a waje ya samota.

“Mahaifinshi ba haka yake yi ba mahaifinshi ya zo nan masallacin a wurin nan ya cewa malam abinda kake koyarwa shi ne gaskiya, anyi shi a nan.

“Saboda haka karsu yadda su bashi wannan daraja da sharaf, wanna hukuma ta janyeta.

Haka kuma malamin ya ce bayyanar Abduljabbar da akidunsa wa’azi ne ga malaman Kano baki daya.

Ya ce Allah ya aiko musu shi ne domin ya nuna musu yadda za su rike Ilimi ba a yi wasarairai dashi ba.

Malam Gumi ya ce idan ana bukatar kai shi kasa to dolene a koma karatun mazahaba domin tantance tasaba da tsakuwa.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending