KANUN LABARAI
Gadar Kofar Nasarawa ce kadai abin alfaharin ‘yan Kwankwasiyya-Gwamnatin Kano

Mukhtar Yahya Usman
Gwanatin Kano ta ce ‘yan Kwankwasiyya sun firgice ne saboda ta ce za ta yi gyara a jikin gadar Kofar Nasarawa da zai amfanar da al’umma.
Kano Focus ta ruwaito Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba ne ya bayyana haka ta cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan rediyo freedom ranar Litinin.
Muhammad Garaba ya ce ‘yan Kwankwasiyya basu da wani abu da za su nuna ko tunkaho da shi da ya wuce gadar.
“Saboda firgita da ‘yan hamayya suka yi, yan PDP yan Kwankwasiyya, saboda babu wani abu da suke da shi da za a iya gani a taba a fadin jihar Kano illa iyaka wanna gadar.

“Wannan gada indakasan rayukansu haka take, saboda haka suka kidime baki dayansu, sukai ta shiga gidajen rediyo sunata kalubalantar abin.
“Mu abinda muke cewa ,ai kaga bayani ne na hankali, bayani ne mai gamsuwa, duk wanda yasan me ya ke yi zakaga cewa koma wace gwamnati ce, kodama gwamnatin su ce da take mulki, indai gwamnati suke ta hakika aka ce wannan abu zai iya kawo hadari, kuma abu na karshe da ya kamata a yi shi ne a yi kaza, na tabbatar indai gwamnati na jama’a ne za su duba su gani.
“Nariga naji duk kalubalen da ake yadadawa na biliyan shida da aka gina wannan gada, idan aka rusheta ina za a samu a sake ginata.
“Amma kamar yadda na fada ai ba cewa nayi gwamnati ta zauna tayi nazarin rahoton, wannan shi ne abu na karshe ba.
“idan har ta kama cewar za a iya gyara wasu daga cikin wuraren da ya tsuke, duk irin wadannan gyare-gyaren idan ta kama za a gyara ba tare da anzo matakin da za a ce an ruguza ba.
“Amma wallahi ni banyi magana ta siyasa ba, kuma banyi tunanin cewa na fadi wanna maganarba, saboda munaso mu shafe ayyukan da Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
