KANUN LABARAI
Gwamnatin Kano ta musanta rushe gadar Kofar Nasarawa
Mukhtar Yahya Usman
Gwamnatin Kano ta ce ko kadan bata da shirin rushe gadar Kofar Nasarawa illa iyaka wasu yan gware-gyare da za yi a jikin gadar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ta cikin shirin ‘Barka da hantsi’ na gidan rediyo freedom ranar Litinin.
Muhammad Garba ya ce ko kadan ba a ce za a rushe gadarba, illa iyaka gyare-gayare da aka ce za a yi a jikin gadar da ake ganin tana bada barazana.
Ya ce, ya yi bayani ne a baya kan halin da gadar ke ciki, inda ya ce masana na nan na hada bayani kan halin da gadar ke ciki, na matsalolin da ake ganin ta samu.
Garba ya ce da zarar sun karbi sakamakon binciken, za su yi amfani da bayanin wajen gyara duk abinda suka bijori da shi.
Idan za a iya tunawa dai, tun a ranar Taladar da ta gabata ne Muhammad Garba ya ce akwai yiwurar rushe gadar sama ta kofar Nassrawa sakamakon zaizayerar da ta fara yi.
Muhammad Garaba ya sanar da hakan ne lokacin da yake karbar kungiyar ‘Ganduje raya Kano yake’.
Ya ce, tuni suka shiga nazari tare da ƙwararru kan irin matsalolin da gadar ke haifar wa ga al’ummar Kano.
Ya kara da cewa gadar ta fara zaizayewa saboda rashin kyawun aikin da aka yi, tana kuma hada cunkoso.
Kwamishinan ya ce, da zarar ƙwararru sun gama nazari a kai, gwamnati za ta duba yiwuwar rushe gadar tare da sake ta.
Sai dai kwamishinan ya ce jama’a basu fahinci abinda kalaman nasa ke nufi ba.
Ya ce za su yi aiki ne da bayanan kwararru, da kuma shawarar da suka bayar, idan ma takama a rushe wani bangare na gadar domin a yi gyara to za a rushe, amma ba rusheta baki dayaba.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.