KANUN LABARAI
Neman matar aure: Hisba ta kafa kwamitin mutane 5 da zai binciki Uba Rimo
Mukhtar Yahya Usman
Hukumar Hisbah ta kafa kwamitin mutane biyar domin bincikar jami’inta Sani Uba Rimo da ake zargi da neman matar auren a wani otal da ke Sabon Gari.
Babban kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheikh Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin zantawa da jaridar Kano Focus ranar Laraba.
Ibni Sina ya ce suna samun rahoton abinda jami’in na su ya aikata suka dauki matakin dakatar da shi nan take.
Ya ce ya kuma kafa kwamitin mutane biyar da za su binciki al’marin domin gano musabbabisa da kuma fede gaskiya.
Idan za a iya tunawa a jiya Talatane jami’an ‘yan sanda deke Nomandsland suka cafke Sani Uba Rimo a wani dakin Otal da ke unguawar Sabongari tare da matar aure.
Hisbah za ta dauki ma’aikatan sa kai 5700
Hisbah ta bukaci masu laifi suyi sallah raka’a 50 kafin a kaisu kotu
Hisbah za ta fara bude kananan ofisoshi a cikin unguwannin Kano
Uba Rimo, jami’in Hisbah ne da ke kula da bangaren hana barance-barace da hana yawon banza a fadin jihar Kano.
Rahotanni sun ce mijin matar ne yakaiwa ‘yan sanda korafin Rimo ya gayyaci matarsa zuwa wani otal a Sabon Gari.
Inda su kuma suka mamayi Otal din suka kuma yi masarar kamashi a dakin tare da matar.
Sai dai Ibn Sina ya ce ba za su yi kasa a gwiwaba wajen daukar matakin da ya da ce ga jami’in nasu, matukar aka sameshi da laifi.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu yada abinda zai zama alkairi ga musulunci da musulmi.
A cewarsa yada irin wannan al’amari ba zai zama kare martabar msulunci ba illa iyaka tozardar da shi a idon wadandan ba musulmi ba.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.