KANUN LABARAI
Mun sasanta ‘yan Sahu ne saboda abin ya shafi ma’aikata-Kungiyar kwadago
Aminu Abdullahi
Kungiyar kwadago ta ce ta shiga tsakanin direbobin Adai-daita Sahu da hukumar KAROTA ne duba da halin garari da al’umma suka shiga musamman ‘yan makaranta da marasa lafiya da sauran ma’aikata da basu da abin hawa.
Kano Focus ta ruwaito cewa shugaban kungiyar a jihar Kano Kwamared Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana haka ranar Laraba a nan Kano
Kabiru Ado Munjibir ya ce duk da cewa ‘yan Sahu basa cikin kungiyar kwadago a dokance amma doka ta basu dammar yin magana akan abubuwan da suka shafi al’umma baki daya.
Ya ce sunyi wa kungiyoyin direbobin adaidaita-sahu alkawarin cewa za su yi aiki tare da sauran kungiyoyin alumma wajen basu shawarwari ta bangaren shugabanci.

“Idan za a iya tunawa a baya, idan kungiyoyin kwadago za su yi zanga-zanga ‘yan Achaba ne a gaba suke ja.
Ba yanzu muka fara wannan alakarba, kawai dai an dan ja da baya ne amma yanzu zamu daukaka ta.
“Mun fahimci cewa akwai matsala a shugabancin yan adai-daita sahu a Kano.
Kungiyar kwadago ta gargadi gwamnatin Kano kan sake yankewa ma’aikata albashi
Yanzun nan: Kungiyar ‘yan sahu ta umarci mambobinta su janye yajin aiki
Yanzu-yanzu: An sulhunta tsakanin jami’an KAROTA da ‘yan Adai-daita Sahu
Da akwai kungiyoyi kusan guda takwas, ta yadda idan suna aiki a kan titi shugabannin basa iya gane hakkikanin ‘yan kungiyar su,” a cewar sa.
Ya kara da cewa za su zauna da shugabannin don fito da wata alama ko kati wanda da zarar angani za a san daga wace kungiya dan Adai-daita-sahu yake.
Ya kuma ce idan har akwai direbobin da suke ganin wani abu ya shige musu duhu, to su garzaya ofishin kungiyar Kwadago za su bincika domin warware matsalar.
A nasa bangaren wani direban Adai-daita Sahu Mustapha Halliru ya zargi hukumar KAROTA da takura musu fiye da sauran masu ababen hawa.
Ya kuma roki hukumar da ta sassauta musu.
Haka zalika ya ce duk da cewa ba duk aka taru aka zama daya ba, amma akwai batagari a cikin direbobin Adai-daita Sahu da ya kamata su gyara dabi’unsu.
Yana mai cewa bai kamata wasu direbobin su dinga barin tarbiyar da suka samu daga gida ba da zarar sun hau kan titi.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
