KANUN LABARAI
Dakatar da kai abinci yankin kudu nasarace ga Arewa-Danmaje
Mukhtar Yahya Usman
Shugaban kungiyar masu kishin arewacin kasar nan(Arewa Concern Citizen Development ) Alhaji Rufa’I Mukhtar Dan Maje ya ce daukar matakin da kungiyar masu fatauncin abinci ta yi na dakatar da kai abinci kudancin kasar nan ya yi kyau matuka.
Kano Focus ta ruwaito Dan Maje ya bayyana hakan ne ya yin da yake zantawa da manema Labarai ranar Litinin a nan Kano.
Ya ce lokaci ya yi da al’ummar Arewacin kasar nan za su farka su su kuma san darajar kansu, su kuma kare martaba da kima na yankinsu.
Ya kara da cewar ikirarin da al’ummar kudu ke yi na cewa dan Arewa ba zai rayu a yankinsu ba ya saba dokar kasa amma hukumomi basu dauki matakin komai ba.
Duk gidan man da aka samu na boye mai da gan-gan za a hukuntashi-Muhyi Magaji
Yajin aikin malaman jami’o’i baraza ne ga ilimi a arewacin kasar nan-Danmaje
Martani ga al’ummar Yarabawa, da batun karfafa hadin kan kasa
Acewar Dan Maje al’ummar Arewa ta kare mutuncin mutanen kudu da ke zaune a yankinta, amma su sun gaza yiwa dan Arewa hakan a nasu yankin.
A don hakan ne ya yi kira ga hukuma da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta biyan diyyar wadanda aka kashe a yankin na kudu ba gaira ba dalili.
Idan za iya tunawa dai tun a watan Fabrairun da ya gabata ne rikici ya barke tsakanin Hausawa da al’ummar yarabawa a kasuwar sayar da kayan gwari ta sasha da ke garin Badin a jihar Oyo.
Lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali har ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 40 da galibin su Hausawa ne.
Sai dai jim kadan bayan faruwar al’amarin ne aka jiyo shugaban hadaddiyar kungiyar masu fataucin kayan abinci da dabbo ta kasa dakta Muhammad Tahiri na ayyana shiga yajin aikin kungiyar.
Muhammad Tahir ya ce ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnati ta biya su diyyar wadanda aka kashe musu.
Ya kuma ce ba za su dawo aiki ba har sai dan Arewa ya san kansa kuma gwamnati ta fahinci mutunci jama’ar Arewa.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.