Connect with us

Hausa

Shekara guda a mulkin Kano, wacce rawa Aminu Ado ya taka

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

A ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2020 ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Aminu Ado Bayero Sarkin Kano na goma sha biyar a dular Fulani.

Kano Focus ta ruwaito nadin Alhaji Aminu Ado Bayero ya biyo bayan tunbuke sarkin Kano na 14 a daular Fulani Malam Muhammadu Sunusi II da gwamnan ya yi.

Gwamnan dai ya tunbuke rawanin sarki Sunusi ne bayan da ya ce baya bin ka’idojin da saurauta da gadar, tare da rashin girmama na gaba da ma wasu dalilan.

Haka kuma bayan tunbukeshi ne gwamnan ya ayyana Aminu Ado a matsayin sabon sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan Kano baki daya.

Wanen ne Aminu Ado Bayero

An haifi sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a rananar 1 ga watan Yulin 1961.

Mahaifinsa shi ne marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, sarki na 13 a daular Fulani, da ya kuma kwashe shekara 51 yana sarautar Kano tun daga shekarar 1963 zuwa 2014.

Aminu Ado Bayero shi ne da na 2 a wurin mahaifinsa, ya yin da Sunusi Lamido Ado Bayero ke zaman babban wansu, sai kuma sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ke biye masa a matsayin da na uku a wajen mahaifinsu.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara karatun Islamiyya a gidan Dabo, inda a nanne ya koyi karatun alkur’ani, fiqhu da sauran litattafan addini.

Haka kuma ya halarci makarantar firamare ta Kofar kudu da ke gidan sarki, da ga nan kuma ya wuce sakandiren gwamnati da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa.

Haka kuma bayan kammala sakadire ne sarki Aminu Ado Bayero ya shiga jami’ar Bayero inda ya karanci fannin jarida.

Bayan ya kammala ne kuma ya shiga makarantar koyon tukin jirgin sama, da ke Birnin Oakland a California da ke kasar Amurka.

Haka kuma ya yi bautar kasa a gidan talabijin na kasa NTA da ke Makurdi.

Sarkin ya fara aiki a matsayin jami’in hulda da jama’a na kamfanin Kabo Air, kafin ya yazama injiniyan cikin jirgi.

Sarautun da ya rike

A shekarar 1990 ne mai martaba sarkin Kano Alhji Ado Bayero ya nada Aminu Ado a matsayin Dan Majen Kano hakimin Dala.

Haka kuma a watan Oktobar wannan shekara ne aka kara daga likkafarsa daga Dan Maje zuwa Dan Buran hakimin Dala.

A shekarar 1992 Alhaji Ado Bayero ya sake daga likkafarsa zuwa Turakin Kano hakimin Dala yayin da a shekarar 2000 aka sake daga likkafarsa zuwa Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

A wannan shekara ne kuma ya zama shugaban shirya haye-hayen Dawaki na masarautar Kano.

Haka zalika sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya sake daga likkafarsa daga Sarkin Dawakin Tsakar gida zuwa Wamban Kano a shekarar 2014.

Hakan ce ta sanya a ka sauya masa gari daga Dala zuwa karamar hukumar Birni.

Haka zalika ya samu karin girma zuwa sarkin Bichi, bayan da gwamnan Kano Abudullahi Ganduje ya gididdiba masarautar Kano a shekarar 2019.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama sarkin Kano a ranar 9 ga watan Maris 2020 bayan da gwamnan Ganduje ya tunbuke sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Ayyukan sarkin cikin shekara guda

Yana daga cikin ayyukan da sarkin ya gudanar tun bayan zamansa sarki shi ne kai ziyara duk wata masarauta da ke kasar nan domin kara karfafa zumunta.

Haka kuma ya samu damar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattauna al’amuran da suka shafi ci gaban Kano.

Ya kuma himmatu wajen baiwa gwamnatin Kano hadin kai domin gudanar da yyukanta yadda ya kamata, ba kamar a baya ba da gwamnatin ta ce masarautar na adawa da ita.

Haka zalika tun bayan zamansa sarki ya halarci bikin saukar karatun alkur’ani na makarantu sama da dari a fadin Birnin Kano tare da bude masallatai.

Hausa

Hisba za ta tilastawa ma’aurata shiga makarantar nazarin zamantakewar aure a Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta ce za ta bude makarantar koyon zamantakewar aure a Jihar Kano cikin , a watan Nuwambar wannan shekara.

KANO FOCUS ta ruwaito babban kwamandan hukumar, Muhammad Haruna Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Freedom.

Ibn Sina ya ce, a matakin farko zabi ne ga wanda ke da sha’awar shiga, amma a nan gaba za su yi kokarin ganin an mayar da shi doka ga duk mai son yin aure a Kano.

“Kaso 75 daga cikin korafin da mu ke karba kan matsalolin aure ne, wannan ne ya sanya muka samar da makarantar don ba da horo.

“Matsalar yawaitar mutuwar aure a kullum karuwa take musamman a Kano, don haka makarantar za ta samar da hanyoyin dabarun koyar da ilimin zamantakewar aure,” cewar Ibn Sina.

Kazalika, kwamandan ya kara da cewa za su shigar da kudiri gaban majalisar dokokin Jihar don tilasta wa ma’aurata shiga makarantar.

Ibn Sina, ya kuma kara da cewa horaswar ba iya mata za ta tsaya ba, har da maza za a basu damar shiga don samun daidaito da raguwar matsalolin.

Matsalar aure a Jihar Kano na ci gaba da zama babbar kalubale musamman kan yadda Hisbah ke fama wajen warware su.

Continue Reading

Hausa

Dalilin da ya sa muke Maulidin shan kauri – Alkarmawi

Published

on

Sheikh Muhammad Nazifi Alkarmawi

Nasiru Yusuf

Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Alkarmawi ya ce ya fara yin walimar Maulidin shan kauri ne don girmamawa ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Malamin ya shaidawa KANO FOCUS cewa kamar yadda yake a al’adar Hausawa idan aka yi kwana biyar da haihuwa akan yi kauri a raba, shi ne shi ma ya za6i yin walimar Maulidin shan kauri bayan kwana biyar da zaman haihuwa.

Ya ce duk abun da za a yi don girmama Annabi halal ne, kuma ba a neman nassi.

Sheikh Muhammad Nazifi Alkarmawi ya ce, kodayake ranar walimar shan kauri ba rana ce ta jawabi ba, amma dai za a ciyar da ruhi darajojin Annabi, kafin ciyar da gangar jiki.

Malamin ya ja hankalin Musulmi kan muhimmacin koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), inda ya ce ba a samun nasara a rayuwa sai an yi koyi da Annabi.

Malam Alkarmawi ya ce kullum da ma ana cikin Maulidi ne, sai dai a watan Maulidi ana haduwa da sauran mutane don a yi murna.

A lokacin Maulidin malamai sun yi jawabai kafin daga bisani aka yi walima da romon ganda da gurasa.

Ga hotunan walimar a kasa:

Continue Reading

Hausa

Rikici na da malaman Kano jarrabawace daga Allah-Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta Kano Sheikh Ibahim Khalil, ya bayyana rikicinsa da malaman da suka yi yunkurin tsigeshi a matsayin wata jarrabawa daga Allah.

KANO FOCUS ta ruwaito malamin ya bayyana hakanne ya yin da ya karbi bakuncin mambobin majalisar kolin addinin musulunci ta kasa da suka ziyarce shi a ofishinsa ranar Asabar.

Malamin ya ce Allah ya yi alkawarin jarraba bawansa don a ga ko zai iya jurwa ko akasin haka

“Allah Ya yi alkawarin jarraba mu a kowanne abu. Abin da ya faru watakila Allah Ne Ya yi niyyar jarraba mu don Ya ga ko da gaske muke a tafarkinsa.

“Saboda haka, na dauki wannan a matsayin jarrabawa, amma Alhamdulillahi, Allah Ya nuna mana tsintsiya madaurinki daya muke, kuma ina rokon Ya yafe mana.

“Ina godiya ga dukkn wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin kan malaman Kano ya hadu, ciki har da wadanda ma ba sa cikin majalisar, amma suna mana fatan alheri,” inji Sheikh Khalil.

Anasa jawabin Malam Jamilu Mu’azu Haidar,  a madadin malaman ya ce sun zo Kano ne don nuna goyon bayansu ga shugabancin nasa.

Malam Jamilu, ya ce sun saurari bayanai daga malaman Kano daban-daban, inda aka ba su tabbacin cewa babu hannun gwamnatin jihar a rikicin.

“Muna kira ga sauran malamai da su ji tsoron Allah su dawo a ci gaba da tafiya tare, karkashin Sheikh Khalil, kamar yadda ake a baya,” inji Malam Jamilu.

Idan za a iya tunawa dai a baya-bayan nan ne wasu malamai a nan Kano suka sanar da tsige Malam Ibrahim Khalil daga mukaminsa.

Haka kuma sun nada Farfesa Abdallah Saleh Fakistan a matsayin wanda zai maye gurbinsa, lamarin da yaki karbuwa a wajen jama’a dama sauran malamai.

Continue Reading

Trending