Connect with us

Hausa

Matasan Arewa ne koma baya a bangaren fasahar sadarwa-Kungiya

Published

on

Aminu Abdullahi

Wata kungiya mai rajin Kawo sauyi a Arewacin Najeriya wato (Arewa Agenda) ta ce matasan Arewa su ne koma baya ta bangaren ammafani da ilimin kimiyya da fasaha idan aka kwatanta da na kudu.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kungiyar Muhammad Dahiru Lawan ne ya bayyana haka yayin taron wayar da kai kan yadda za ayi amfani da fasahar zamani don dogaro dakai ranar Lahadi a nan Kano.

Ya ce rashin wayewa ta sanya da yawa daga cikin matasan Arewa basa bibiyar shafukan da aka wallafa a yanar gizo domin bada horo da kuma tallafi akan lamuran da suka shafi fasahar sadarwa.

Ya ce da yawan matasan kudancin kasar nan sun yi nisa wajen samun kudi ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Muhammad ya ce akwai bukatar malamai da shugabanni a Arewa su dinga daukar nauyin wayar da kai, da daukar nauyin yiwa matasa rijista musamman wadanda ke zaune a karkara.

“Akwai fasahohi dayawa kamar kirkirar manhajoji ko Web Designing da mutum zai iya dogara da su a matsayin hanyar samun rufin asiri.

“Nan gaba kadan duniya za ta canza, mutane da yawa za su rasa ayyukan yi saboda fasahar yanar gizo kuma Indai bamu rungumi wannan fasahar a yankin nan ba to za a barmu a baya.

“Akwai gurare da NITDA ta samar a nan Kano da idan kana da fasaha zakaje kai tsaye kyauta kayi duk abinda kake so,” a cewar sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Hotuna: Sarkin Kano ya halarci taron Maulidi

Published

on

Aminu Ado Bayero

Nasiru Yusuf

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya halarci taron Maulidi da aka yi Gidan Rumfa (Gidan Sarki) ranar Litinin.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara ne ya gabatar da karatu a lokacin Maulidin.

Maulidin ya samu halartar manyan Hakimai da malamai da sauran jama’a.

Ga sauran hotunan taron Maulidin.

Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara

 

Continue Reading

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Trending