Connect with us

Hausa

An sace mutane 12 ‘yan Kano a Kaduna

Published

on

Aminu Abdullahi

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane goma sha biyu ‘yan gida daya, kuma ‘yan asalin jihar Kano a karamar hukumar birnin Gwari dake jihar Kaduna. 

Kano Focus ta ruwaito cewa iyalan, dukkaninsu mazauna unguwar Garu ne dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Rahotannin sunce an sace su ne a hanyarsu ta dawowa Kano, bayan da suka halarci biki  a jihar  Neja.

Kimanin kwanaki takwas kenan da sa ce su, amma har yanzu basu samu ‘yanci ba.

Wani da matarsa da ‘ya’yan sa biyu ke cikin wadanda akayi garkuwa dasu, Shehu Yahya ya ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci da su biya naira miliyan saba’in.

Sai dai ya ce daga baya sun rage zuwa naira miliyan goma, inda suka ce daga wannan ba za su kara rage ko sisi ba.

Ya ce wadanda aka sace sun hada da Safiya Shehu mai shekaru 60, sai Asma’u Yahya ‘yar shekara 75, da Hadiza Abdullahi mai shekara 90, da Talatu Abdullahi ‘yar shekara 85 ,da kuma Habiba Auwalu mai shekara 35.

Sauran sune Habiba Auwalu, da Fatima Ali, da Khadija Usman, sai Saifullahi Usman, da Khadija Abdullahi, sai Hamisu Adamu, da kuma direban motar mai suna Abubakar Na’ibawa.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun kira su a waya, inda suka ce sun kashe mutum guda a cikin mutane goma sha biyu a don haka a biya kudin fansa a dauki gawar sa.

“Mata goma ne cikin wadanda suka kama ma za biyu, to yanzu sunce sun kashe mutum guda daga cikin su.

“Kullum sai sun kira mu a waya sun saka mana kukan su da yadda suke nada musu na jaki, muna rokon hukuma da ta shiga lamarin,” a cewar sa.

Hamisu Garu, ya ce sun sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta kasa da gwamnatin jihar Kaduna amma har  yanzu ba a kubutar dasu ba.

Ya ce mahaifiyyarsa da kannen sa guda biyu duk suna hannun masu garkuwa da mutanen kuma babu wanda aka saka a cikin su.

Sai dai da muka tuntubi runduanr ‘yan sandan jihar Kano kan al’amarin ta ce bata da hurumi a kai.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ce ke da hurumi kan al’amarin.

Haka zalika da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ta ce za ta bincike al’marin.

Mai Magana da yawun rundunar Muhammad Jalige ya ce da zarar sun kammala bincike za su sanar da mu halin da suke ciki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending