Connect with us

Hausa

Neman suna yasa Ummi Zee Zee ta yi ikirarin kashe kanta

Published

on

Aminu Abdullahi

Al’umma na cigaba da nuna shakku kan kalaman tsohuwar jarumar Kannywood Ummi Ibrahim  Zee Zee na cewar damfarar da akayi mata ne yasa taso halaka kanta.

Inda da dama ke ganin jarumar ta furta kalaman ne kawai domin neman suna, tunda dai tauraruwarta ta disashe.

Kano Focus ta ruwaito cewa Zee Zee ‘yar asalin jihar Barno yar shekara 32 ta ta ce taso kashe kanta ne bayan da wani inyamuri ya damfareta  Naira miliyan 450.

A wata hira da akayi da jarumar ta ce ta wallafa batun  za ta kashe kantane sakamakon damfarar da wani Inyamuri yayi mata akan kasuwancin danyan man fetur.

Sai dai wasu mutane na ganin jarumar tayi hakane kawai don neman suna duba da yadda tauraruwarta ta disashe.

“Abin Tambaya, a baya wanne irin kasuwanci sukayi da mutumin kuma kasuwanci na wadannan makudan kudade ba lauya a ciki,” a cewar Alhassan Auwal.

Ya kara da cewa ga duk mai tunani bai kamata ya yarda da dalilan tsohuwar jarumarba domin kuwa tsagwaron karya ce a cikin sa.

“Kasuwanci na irin wadannan kudade, shin ya ya sunan kamfaninta da tayiwa rijista, kuma shi abokin kasuwancin nata bashi da kamfani mai rigista ya kamata a kallo jawabin ta da Idon basira.

“Ta fadi hakanne kawai don ta motsa tauraruwarta, duba da yadda aka manta da ita kaga ko banza yanzu jaridu sun cika da labarin ta,” inji shi.

Ahmad Umar cewa ya yi idan har gaskiyane batun da Zee Zee tayi to bai kamata taki sanarwa da jami’an tsaro halin da ake ciki ba.

“Wacce ta ce za ta kashe kanta kuma ta ce kada a tambayeta dalili amma kuma take maganar komawa hakar fim.

“Lokacin ta ya wuce duk irin abinda zatayi da zai jawo cece-kuce ba zai sa ‘yan kallo su karkata zuwa gare ta ba.

Zahra ‘u Umar ta ce ba abin mamaki bane dangane da dalilan da ta bayyana, kasancewar da yawan mutane kanyi amfani da hanyoyi daban-daban domin neman daukaka.

Matsalar tsaro: ‘Yan wasan Hausa a Kano na caccakar shugaba Buhari

Hausa fim: Yaron da yazo Kano daga Adamawa don ganin Ado Gwanja

Yanzu-yanzu: Kungiyar musu shirya-fina-finan Hausa a Kano ta kori Rahama Sadau

Ta kara da cewa koda an damfari jarumar to kudin bai kai adadin yadda ta fadaba, domin kuwa babu wanda zai yi irin wannan kasuwancin ba tare da shaida ko lauyoyi ba.

“A jawabinta ta kasa fadan sunan mutumin ko sunan da yake amfani dashi a kafafen sada zumunta duk da ta ce yayi blocking din ta.

“Sanan ta ce bata sanarwa ‘yan sanda halin da ake ciki ba shin haramtaccen kasuwanci sukeyi kenan,” a cewar ta.

Zahra’u ta ce akwai bukatar jarumar ta sake fito da wata hanyar ta neman suna, amma ba wannanba, wadda ko karamin yaro ne yaji yasan ba gaskiya bane,” a cewar ta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending