Connect with us

Hausa

Yin buda baki da taba sigari na tauye ladan azumi-Sheikh Abdallah G/Kaya

Published

on

Zulaiha Danjuma

Babban Malamin Addinin Islama a nan Kano sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya ya ce yin buda baki da taba sigari, ko wiwi ko wani abun shaye-shaye isgilanci ne ga addini.

Dakta Abdallah Gadon Kaya ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Kano Focus ranar Litinin a nan Kano.

Wani bincike da Kano Focus ta gudanar ta gano yadda al’umma da dama a nan Kano ke fara yin buda baki da taba sigari, ko kuma wiwi, maimakon dabino da ruwa da aka saba.

Sai dai malamin ya ce shari’a ta gama yin bayanin mai yakamata wanda ya yi azumi ya yi buda baki dashi.

“Annabi ya karantar damu cewa idan mutun ya yi azumi zai sha ruwa, ya yi budan baki da dabino, dabinon ma sai da aka ware wanne iri.

“Annabi yana fara shan ruwa da danyen dabino, idan bai samuba yakan nemi ruwa yasha.

“Anan shari’a ta nuna mana mai ya kamata musulmi ya yi buda baki dashi, shi ne dabino ko ruwa”

“Malamai kuma suka kara da cewa babu laifi idan mutum bai samu wannan ba ya samu wani dan itace ya yi budan baki da shi”

Haka kuma malamin ya ce ga wadanda ke yin buda baki da kayan shaye-shaye ladan azumin su na tabuwa

“Yin buda baki da wani abun shaye-shaye taba sigari ko wiwi yana iya taba ladan mutun, kuma hakan ya saba wa abin da annabi yazo da shi”

“Yin haka dai-dai ne da ace mutun ya yi buda baki da giya, haramun ne, da giya, da taba ko wiwi duk hukuncin su daya duk haramun ne”

“A takaice wanda ya yi buda baki da wadannan  abubuwa ya yi buda baki da abinda yake haramun”

Ya kuma ja hankalin matasa da al’umma baki daya su rike addinin su kuma su kiyaye yin abubuwan daya haramta

A cewarsa wadanda ke sabawa umarnin Allah su kiyaye kada fitina ta samesu ko azaba me radadi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending